Zan Jingine Siyasa a 2023 Domin In Koma Aikin Tallafawa Mutane, Gwamnan Arewa
- Gwamna Masari na jihar Katsina yace da zaran ya kammala wa'adin mulkinsa a 2023 zai koma tallafawa mabuƙata
- Masari yace tallafawa mutane shine hanyar da zata sa kowane mutum ya saka wa al'ummarsa da shi
- Gwamna ya kaddamar da gidauniyarsa kuma ya raba keken guragu 200 ga naƙasassu daban-daban
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake jaddada aniyarsa ta jingine siyasa da zaran ya kammala wa'adinsa a 2023, kamar yadda dailyyrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Dumi-Dumi: Dalibai Biyu Daga Cikin Wadanda Aka Sace a Bethel Baptist Kaduna Sun Gudo Daga Hannun Barayi
Gwamnan yace zai koma aikin tallafawa marasa ƙarfi domim maida ritayar da yayi abun tunawa a koda yaushe.
Masari ya bayyana hakane a wurin kaddamar da gidauniyarsa, AMAYEF, wanda ya gudana a Katsina ranar Alhamis, kamar yadda pm news ta ruwaito.
Masari yace: "Yayin da shekarar 2023 ke ƙara gabatowa, na zaɓi jingine siyasa kuma zan koma tallafawa mabuƙata da karawa matasa karfin guiwa. Wannan shine ainihin abinda aka kafa gidauniyar dominsa."
"Matasa suna da babbar rawar da zasu taka wurin saita goben ƙasar nan, musamman a wannan matsanancin yanayin da muke ciki."
"Samun matasa nagari a kowace irin al'umma ya na da alaƙa da irin damar da aka samar musu, kuma manyan mutane ya kamata su rinka yin haka domin saka wa mutanen su."
"Wannan shine dalilin kafa gidauniyar Aminu Bello Masari, a matsayin ɗaya daga cikin gudummuwa ta ga al'umma." inji Masari.
KARANTA ANAN: Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura
Masari ya yi kira ga masu arziki
Gwamna Masari ya yi kira ga masu kuɗi a ƙasar nan da su tallafawa al'ummarsu musamman marayu, mata, matasa da kuma masu naƙasa domin dogaro da kansu.
Masari ya ƙara da cewa gidauniyar zata yi aiki tuƙuru wajen samar wa matasa aikin yi domin rage zaman kashe wando a cikin al'umma.
A lokacin kaddamar da gidauniyar, an raba keken guragu ga mutane masu naƙasa daga ƙananan hukumomi 34 dake faɗin jihar.
A wani labarin kuma Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC
Shugaban ADC ta kasa, Mr. Nwosu, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan wasu gurbatattun yan siyasa zasu koma APC.
Jam'iyyar ADC ita ce wadda ta zo na uku a zaɓen 2019 da ya gabata a yawan kuri'u.
Asali: Legit.ng