Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna

Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna

  • Rundunar yan sanda ta sanar da sake samun nasarar kubutar da ɗaliban Bethel Baptist biyu
  • Rundunar tace an kuɓutar ɗaliban ne a wani yanki dake kan hanyar Kaduna-Abuja
  • A makon da ya gabata jami'an yan sanda suka kubutar da ɗalibi ɗaya, yanzun ɗalibai uku kenan aka kubutar

Gwarazan jami'an yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar Bethel Baptist dake karamar hukumar Chukun, jihar Kaduna, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hotunan Wani Gwamna da Ya Rungumi Sana'ar Hada Takalmi da Takalman da Yake Haɗawa

Yan sandan sun kuɓutar da ɗaliban ne ranar Laraba da yamma a yankin Rijanna dake kan hanyar Kaduna-Abuja, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Rahoton dailytrust ya bayyana cewa ɗaliban ne suka gudo daga inda ake tsare da su, inda daga bisani yan sanda suka gano su a cikin daji, suka dakko su zuwa asibiti.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Yan Sanda Huɗu Tare da Wasu Mutane da Dama a Enugu

Jami'an yan sanda
Da Duminsa: Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hukumar makaranta ta tabbatar

Wani malamin makarantar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da kuɓutar daliban ranar Alhamis.

"Eh, ɗalibai biyu sun gudo daga hannun yan bindigan ɗa suka sace su," inji majiyar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ya shaidawa manema labarai cewa an kai ɗaliban biyu sashin kula da lafiya na rundunar yan sanda, inda ake duba lafiyarsu a halin yanzu.

Yace: "A halin yanzun ana duba lafiyarsu a sashin kula da lafiya na hukumar yan sanda."

Yan bindiga sun sace ɗalibai 121

A ranar 8 ga watan Yuli, wasu yan bindiga suka sace ɗalibai 121 a ɗakin kwanan ɗalibai na makarantar sakandiren Bethel Baptist dake karamar hukumar Chikun.

Jami'an yan sanda sun kuɓutar da ɗalibi ɗaya a makon da ya gabata, yayin da suka sake samun nasarar kuɓutar da wasu biyu ranar Laraba.

KARANTA ANAN: Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

Sai dai, ɓarayin da suka sace ɗaliban sun nemi a haɗa musu naira miliyan N60m kuɗin fansa kafin su sako yaran dake hannunsu.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai

Yan bindiga sun harbe jariri ɗan wata uku kacal har lahira tare da wasu mutum 12 a hari daban-daban a wasu ƙauyukan karamar hukumar Guma, jihar Benuwai.

Yan bindigan sun buɗe wuta kan matafiya a hanyar Uikpam–Umenger da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutum biyar, cikinsu harda jariri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel