Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura

Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura

  • Wa'adin da sarkin Muri, Abbas Tafida, ya baiwa fulani makiyaya a ranar Idi ya jawo cece-kuce
  • Sarkin dai ya baiwa makiyayan kwanaki 30 su bar dazuzzukan dake yankin jihar Taraba
  • Kungiyar miyetti Allah, wadda ta saba kare makiyayan ta yi shiru bata ce komai ba game da lamarin

A ranar Talata, ranar da al'ummar musulmi suka yi sallah, Sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida, ya baiwa fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar dazukan jihar Taraba, ko su daina garkuwa da mutane, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC

Wannan kalaman na basaraken ya jawo cece-kuce tsakanin jama'a duk da ana ganin cewa sarkin yayi jawabin ne a fusace.

Kalaman sarkin Muri sun bar baya da kura
Maganar da Sarkin Muri Ya Yi Ranar Sallah Kan Fulani Makiyaya Ta Bar Baya da Kura
Asali: UGC

A jihar Taraba, jama'a na cigaba da faɗin albarkacin bakinsu game da wannan magana ta sarkin nasu.

Sarkin yace: "Duk da cewa muma fulani ne kamar su, amma ba zamu zauna muna kallo sun cigaba da mana ɗauki ɗai-ɗai ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC

KARANTA ANAN: Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari

Gwamnatin Taraba ta yi gum game da kalaman

Duk wani ƙoƙari na jin ta bakin gwamnatin jihar Taraba dangane da wa'adin da sarkin ya baiwa makiyaya ya ci tura.

Hakazalika, a ɓangaren fulani, ƙungiyar miyetti Allah ta ƙasa, wacce ta saba kare fulanin idan aka taba su, ita ma ta yi shiru ba tace komai ba.

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna

Gwarazan jami'an yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar Bethel Baptist dake karamar hukumar Chukun.

Yan sandan sun kuɓutar da ɗaliban ne ranar Laraba da yamma a yankin Rijanna dake kan hanyar Kaduna-Abuja.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel