Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC

Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC

  • Shugaban ADC ta kasa, Mr. Nwosu, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan wasu gurbatattun yan siyasa zasu koma APC
  • Jam'iyyar ADC ita ce wadda ta zo na uku a zaɓen 2019 da ya gabata a yawan kuri'u
  • Yace manyan yan siyasa na komawa APC ne domin a shafe irin ta'asar da suka aikata

Shugaban jam'iyyar ADC ta ƙasa, Mr. Ralphs Okey Nwosu, yace yan siyasa masu cin hanci da rashawa zasu koma APC ba da jimawa ba.

KARANTA ANAN: Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari

Nwosu, wanda ya yi fira da ThisDay a Awka, ranar Laraba, ya bayyana cewa ba abun mamaki bane dan yan siyasar dake cin hanci sun koma jam'iyya mai mulki APC, musamman yan majalisun tarayya.

Shugaban ya yi dana sanin jam'iyyarsa, wanda take matsayi na uku a manyan jam'iyyun ƙasar nan, ta rasa wasu daga cikin yan majalisunta zuwa APC.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

A cewarsa, jam'iyyar APC ba ta boye manufofinta na jawo hankalin gurbatattun yan siyasa su koma cikinta.

Shugaban ADC, Mr. Ralphs Okey Nwosu
Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

ADC ce jam'iyya ta uku a Najeriya

Wani ɓangaren jawabinsa, Yace: "A lokacin zaɓen 2019 jam'iyyar mu ce tazo na uku a ƙuri'un da aka kaɗa. Mun samu yan majalisun dokoki 15, sannan mun samu yan majalisun tarayya bakwai, amma abun takaici biyu sun fice."

"Munsan yanayin yadda siyasar Najeriya take, da zaran yan siyasa sun shiga ofis, gurbatattun cikinsu zasu aikata gurbataccen aikinsu, daga nan sai su fara neman inda zasu fake."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Yan Sanda Huɗu Tare da Wasu Mutane da Dama a Wani Gumurzu

"APC na ta yaɗawa ko ina cewa da zaran ka shiga cikinta to an yafe maka dukkan laifukan da ka aikata. Ba ruwansu da laifinka, bukatarsu ka koma jam'iyyar."

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya

Gwarazan jami'an yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar Bethel Baptist dake karamar hukumar Chukun.

Yan sandan sun kuɓutar da ɗaliban ne ranar Laraba da yamma a yankin Rijanna dake kan hanyar Kaduna-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel