Hukumar Ganduroba Ta Yi Magana Kan Halin da Sheikh AbdulJabbar Yake Ciki a Gidan Yari
- Hukumar gandurobobi ta jihar Kano ta musanta rahoton dake yawo cewa Sheikh Abduljabbar bashi da lafiya
- Hukumar tace malamin da saura fursunonin dake karkashin hukumar suna cikin koshin lafiya
- Kakakin hukumar reshen jihar Kano, DSC Musbahu, Shine ya bayyana haka a Kano
Hukumar jami'an dake tsaron gidan gyaran hali ta jihar Kano, ta musanta rahoton dake yawo cewa sheikh Abduljabbar Kabara yana cikin mawuyacin hali a gidan yari, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Hallaka Yan Sanda Huɗu Tare da Wasu Mutane da Dama a Wani Gumurzu
Shehin malamin wanda ya yi ƙauran suna wajen kawo maganganun dake jawo cece-kuce yana gidan yari biyo bayan umarnin kotu.
Kakakin hukumar, DSC Musbahu K/Nassarawa, yace rahoton dake yawo cewa malamin bashi da lafiya ƙaryane, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Yace: "An jawo hankalin hukumar mu reshen jihar Kano kan wasu ƙarerayi da ake yaɗawa cewa, Sheikh Abduljabbar Kabara, wanda yake tsare a hannun mu, yana cikin matsananciyar rashin lafiya."
Malamin yana cikin ƙoshin lafiya
DSC Musbahu ya ƙara da cewa shehin malamin tare da sauran yan fursuna dake hannunsu, suna cikin ƙoshin lafiya.
Yace: "Muna kira ga mutane da su yi watsi da wannan karyar da bata da tushe ballantana makama, wadda aka shiryata domin wani dalili."
"Muna tabbatar wa al'umma cewa Sheikh, tare da sauran yan fursuna dake tsare a gidajen yarin mu suna cikin ƙoshin lafiya."
KARANTA ANAN: Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna
"Kuma hukumar mu tana bada muhimmanci matuka ga lafiyar dukkan yan fursuna dake hannunta."
A wani labarin kuma Hotunan Wani Gwamna da Ya Rungumi Sana'ar Hada Takalmi da Takalman da Yake Haɗawa
Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia , ya bayyana takalmin da ya haɗa da hannunsa a matsayinsa na ɗalibin makarantar Aba-based Footwear Academy.
A wata fira da gwamnan yayi da manema labarai, ya nuna takalmin sandal da ya haɗa dakansa yayin da yake murmushi a fuskarsa.
Asali: Legit.ng