Da dumi-dumi: Hankula sun tashi sosai yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon kwalara ya yi muni a Abuja

Da dumi-dumi: Hankula sun tashi sosai yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon kwalara ya yi muni a Abuja

  • Karamar Ministar Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu ta bayyana cewa akalla mutane 60 ne suka mutu sakamakon barkewar annobar kwalara zuwa yanzu a babbar birnin tarayyar kasar
  • Har ila yau, yawan wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun tashi daga 604 zuwa 698 cikin awanni 72
  • Sai dai Aliyu ta tabbatar da cewar gwamnati za ta dauki matakin da ya kamata domin dakile ccutar

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar kwalara a Babban Birnin Tarayya (FCT) ya haura 60, kamar yadda karamar Ministar Abuja, Dakta Ramatu Tijjani Aliyu, ta bayyana.

Cutar kwalara ta fara ɓarke ne a cikin karamar Hukumar Abuja a ranar 23 ga Yunin 2021, inda ta kashe aƙalla mutum bakwai daga cikin 91 da ake zargi sun kamu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Aliyu, ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a ci gaba da wayar da kan al’umma kan cutar kwalara da sauran munanan cututtukan gudawa da suka barke a yankunan Pyakasa da Gwagwa a cikin babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Da dumi-dumi: Hankula sun tashi sosai yayin da yawan wadanda suka mutu sakamakon kwalara ya yi muni a Abuja
Mutane sun mutu a garuruwa da dama Hoto: Directorate of Peacekeeping Force Headquarters in Abuja
Asali: Facebook

Ta kuma bayyana cewa wadanda ake zargin sun kamu da cutar sun tashi daga 604 zuwa 698 cikin awanni 72.

A cewar mai taimaka wa Ministan kan harkokin yada labarai, Mista Austin Elemue, Aliyu ta samu wakilcin Babban Sakataren Cibiyar Kula da Lafiya a Firamare ta birnin tarayya, Dokta Iwot Ndaeyo.

Ta bayyana cewa karamar hukumar Abaji ta samu mutane uku da ake zargin sun kamu, babu wanda ya mutu, karamar hukumar Abuja Municipal (AMAC) an samu mutum 281 da ake zargin sun kamu tare da mutuwar 22, yayin da karamar hukumar Bwari aka samu mutum 134 tare da mutuwar 22.

Har ila yau, karamar hukumar Gwagwalada an samu mutane 220 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane tara; Kuje yana da mutane 23 da ake zargin sun kau tare da mutuwar mutum hudu sannan kuma Kwali ya kasance da mutane 37 da ake zargin sun kamu tare da mutuwar mutane uku.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

Ministar, wacce ta ce wannan mummunan yanayin ba abun yarda bane, ta ba da tabbacin cewa gwamnatin ba za ta dunkule hannayenta tana kallon mazauna garin suna mutuwa ba tare da wani taimako domin dakile cutar ba.

Jaridar Punch ta ruwaito ministan tana cewa:

“Gwamnatin ba za ta nade hannuwanta ba tana kallon mazauna garin suna mutuwa ba tare da wani taimako ba game da cututtukan da za a iya kiyayewa. Dole ne mu dauki dukkan matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar.”

Hakanan, Shugaban Karamar Hukumar Abuja Municipal (AMAC), Hon. Abdullahi Adamu Candido, ya sake nanata kudirin majalisarsa na dakile yaduwar cutar a cikin al'umma.

A wani labarin na daban, gwarazan jami'an yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai guda biyu daga cikin waɗanda aka sace a makarantar Bethel Baptist dake karamar hukumar Chukun, jihar Kaduna, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya

Yan sandan sun kuɓutar da ɗaliban ne ranar Laraba da yamma a yankin Rijanna dake kan hanyar Kaduna-Abuja, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Muhammed Jalige, ya shaidawa manema labarai cewa an kai ɗaliban biyu sashin kula da lafiya na rundunar yan sanda, inda ake duba lafiyarsu a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng