Cutar kwalara ta barke a Abuja, mutane 604 sun kamu, 54 sun riga mu gidan gaskiya
- Cutar kwalara ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 54 a yankuna badan-daban na Babban birnin tarayya
- Hakazalika, ana zargin cewa, akalla mutane 604 ne suka kamu da cutar ta kwalara cikin kankanin lokaci
- Wannan na zuwa ne daga bakin karamar ministar babban birnin tarayya, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu
Karamar ministar FCT, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ta ce kananan hukumomi shida a garin sun samu mutane 604 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara inda mutane 54 suka mutu.
Ta fadi haka ne lokacin kaddamar da shirin wayar da kan al'umma game da cutar kwalara da sauran cututtukan da suka barke a yankin, Daily Trust ta ruwaito.
Ramatu, wacce ta gabatar da bikin kaddamarwar a fadar Agora na Zuba, HRH Mohammed Bello Umar, ranar Asabar, ta nuna damuwa kan karuwar adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar kwalara.
KARANTA WANNAN: Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47
A cewar ta, sama da al'ummu 120 ne ke cikin lamarin tsakanin kananan hukumomin shida tare da AMAC da ke da mafi girman lamarin sai kuma Gwagwalada da karamar hukumar Bwari.
Don haka, ta yi kira da a kula da tsaftar jiki da kuma kwashe shara da datti yadda ya kamata, bin kyawawan hanyoyin wanke hannu da amfani da tsaftataccen ruwa, wanda ta ce hanya ce ta dakile yaduwar cutar a cikin yankin.
Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance
A kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a kauyen Koya dake karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano bayan zargin barkewar cutar amai da gudawa a yankin.
Dagacin kauyen, Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai inda yace annobar ta fi shafar mata da kananan yara.
Mazauna kauyen da suka zanta da manema labarai sun ce wadanda cutar ta shafa suna ta kwarara amai da gudawa.
KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam
Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17000 a sansani a jihar Borno
A wani labarin, Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta ce an haifi jarirai 17,053 a sansanonin 'yan gudun hijira na Jihar Borno kakai cikin shekaru uku, BBC Hausa ta ruwaito.
Kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai suna International Organisation for Migration (IOM), ta fada wa kamfanin labarai na NAN cewa an haifi yaran ne a sansani 18 da ke jihar, wadanda kuma aka yi wa rajista daga 2019 zuwa watan Mayun 2021.
Mista Frantz Celestin wanda shi ne shugaban IOM, ya ce sun hada gwiwa da hukumar kidaya ta Najeriya da kuma asusun yara na MDD domin sama wa jariran takardun haihuwa.
Asali: Legit.ng