'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

  • Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari wani yankin jihar Kaduna, sun sace wasu mutane da shanu
  • Hakazalika sun hallaka wani mutum bayan aikata barnar da suka aikata a yankin na jihar Kaduna
  • Rahoto ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata, 17 ga watan Yuli

'Yan bindiga sun kashe wani mutumin kauye tare da yin garkuwa da mutane 7, ciki har da mata uku a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Anguwar Gajere dake karkashin yankin Kutemashi na karamar hukumar, a ranar Asabar 17 ga watan Yuli.

An kuma gano cewa 'yan bindigan sun sace shanu sama da 50 daga kauyen.

KARANTA WANNAN: Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Labari mai zafi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace mata
'Yan bindiga | Hoto: dailytrust.com.ng
Asali: Twitter

Wani mazaunin yankin, Mohammed Birnin Gwari, ya shaida wa Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa ’yan bindigan sun zo ne a kan babura da misalin karfe 1 na rana.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Mohammadu ya ce:

"'Yan bindigan sun sace mata uku, maza hudu da shanu da dama bayan sun kashe mutum daya,"

Wani tsohon Kansilan yankin, Adamu Kutemashi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai, rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Jalige Mohammed, ya yi alkawarin ba da bayanai daga baya.

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro a Igangan

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

KARANTA WANNAN: An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Sojojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, sun kwato makamai

A wani labarin, Dakarun sojin saman Najeriya sun lalata manyan motocin bindiga guda uku mallakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP yayin da suke tsallaka hanyar Damaturu zuwa Maiduguri domin aikata barna kan mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis kan ayyukan sojoji a cikin makonni biyu da suka gabata, Mukaddashin Daraktan, Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Brig Benard Onyeuko, ya ce sojojin sun kashe duk wadanda ke cikin motocin.

Onyeuko ya bayyana cewa, sojojin na sama, wadanda suka gudanar da ayyukan ta amfani da jirage masu saukar ungulu NAF Mi-35, sun yi aiki ne a lokacin da suka samu kiran gaggawa tare da tabbatar da cewa an kwato dukkanin makaman ‘yan ta’addan a yayin samamen.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsageru Sun Kai Hari Banki, Sun Sheke Dan Jarida da Wasu Mutum 2

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.