Yan Bindiga Sun Hallaka Yan Sanda Huɗu Tare da Wasu Mutane da Dama a Wani Gumurzu
- Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kashe yan sanda huɗu tare da wasu mutum biyu
- Maharan sun kaiwa wurin binciken abun hawa na yan sanda hari wanda ke Obeagu-Amechi, jihar Enugu
- Hukumar yan sanda ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan lamarin
Aƙalla jami'an yan sanda huɗu aka kashe a wani hari da yan bindiga suka kai wurin binciken abun hawa dake yankin Obeagu-Amechi, ƙaramar hukumar Enugu ta kudu, jihar Enugu, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Karin Bayani: Gwarazan Yan Sanda Sun Kubutar da Wasu Daga Cikin Daliban Bethel Baptist Kaduna
Duk da cewa hukumar yan sanda ba ta faɗi adadin waɗanda suka mutu ba, amma wani mazaunin yankin yace yaga gawar yan sanda huɗu bayan harin.
Hakanan wasu mutum biyu da hanya ta biyo da su, cikinsu harda wani Fasto sun rasa rayuwarsu sanadiyyar harin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Jami'ai sun kashe yan bindiga
Yan bindigan sun sake kai hari jim kaɗan bayan faruwar wancan a gadar Inyaba dake kan hanyar Uno-Amodu – Umueze Amechi, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa aƙalla yan bindiga uku yan sanda suka hallaka a wurin, waɗanda aka sanar da su cikin gaggawa kuma suka kawo ɗauki.
Ruwan wutar da aka yi yayin harin ya bar mutane da dama dake yankin cikin raunuka, sannan maharan sun cinna wa motar sintirin yan sanda wuta.
KARANTA ANAN: Hotunan Wani Gwamna da Ya Rungumi Sana'ar Hada Takalmi da Takalman da Yake Haɗawa
Yan Sanda sun fara bincike
Kakakin yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe, wanda ya tabbatar da kai harin, ya bayyana cewa:
"Bayanai dangane da musayar wuta da ta faru da yammacin ranar 21 ga watan Yuli, wanda wasu yan bindiga suka kaiwa jami'n yan sanda a wurin bincike dake Obeagu-Amechi, yana da rikitarwa."
"Amma a halin yanzu mun fara gudanar da bincike kan ainihin abinda ya faru, kumu zamu sanar a hukumance."
A wani labarin kuma Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC
APC ta sha alwashin fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023 wanda kowa zai amince da shi.
Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar, Sen. John Akpanudoehede, shine ya faɗi haka yayin martani ga PDP.
Asali: Legit.ng