Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya
- Tsohuwar minista ta bukaci a ba mata dama su nuna kokarinsu wajen kai Najeriya tudun mun tsira
- Ta ce yanzu lokaci ya yi da mata ya kamata su yi turjiya dole a basu mulki a bangarori daban-daban
- Ana ci gaba da cece-kuce game da zaben 2023 mai zuwa, yayin da 'yan siyasa ke tufa albarkacin bakinsu
Wata tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Iyom Josephine Anenih, ta bukaci mata a kasar da su zama "masu turjiya" don samun amincewa da nasarar cin zaben shugaban kasa, gwamna da sauran zabuka, Daily Trust ta tattaro.
Misis Anenih ta yi magana ne a wani taro da Gidauniyar Dinidari ta shirya tare da hadin gwiwar Heinrich Boll Stiftung, mai taken: “From the Streets to the Parliament: Empowering Women’s Political Power in Nigeria.”
KARANTA WANNAN: Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade
Ta ce:
“A ko yaushe ina gaya wa mata, lallai ne ku zama 'yan turjiya. Ba za ku iya cin nasara ba idan ku ba masu turjiya ba ne. Dole ne ku yi turjiya ga tsarin.
"Ku yake su (maza) sannan ku yi nasara, kuma lokaci ya yi da matan Najeriya za su tashi don karbar mukamai na jagoranci a duk fadin kasar."
A jawabinta, shugabar mata ta APC, Stella Okotete, ta ce za a iya samun wakilcin mata daidai a harkokin kasa ne ta hanyar samun isassun kudade.
Okotete ta ce:
“Ba tare da kudi ba, mata ba za su iya samun madaidaicin matsayi a fagen siyasa ba, amma idan muka ci gaba, ya kamata mu sauya kanun labarin. Mata su fito su tallafawa mata.”
Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana manya kan batun
Wani matashi dan shekaru 35 da ke neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC a jihar Kano, Malam Aminu Sa’idu, a jiya ya gana da mataimaka na musamman (SAs) ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje don sanar da su burinsa.
Da yake magana da Daily Trust bayan ganawar, matashin ya ce yana daga cikin shawarwarin da yake bi gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Ya kuma ce ganawar ta yi daidai da kudirin dake rajin ba matasa damar a dama dasu a mulki na"Not Too Young to Run", da kuma dabarun fadada aniyarsa zuwa dukkan sassan kasar.
KARANTA WANNAN: Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno
Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah
A wani labarin, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa sojojin da suka ji rauni da ke yaki a yankin tallafin naira miliyan 10 a jiya Talata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne a yayin liyafar cin abincin rana da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Manjo Janar Farouk Yahaya ya shirya a Barikin Maimalari da ke Maiduguri.
Gwamna Zulum ya yaba wa dakarun kan jajircewarsu da kuma jaddada alkawarin gwamnatinsa na ci gaba da ba su goyon baya har a cimma nasara a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin.
Asali: Legit.ng