Hotunan Wani Gwamna da Ya Rungumi Sana'ar Hada Takalmi da Takalman da Yake Haɗawa
- Gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya nuna wa yan Najeriya irin takalmin da ya iya haɗawa
- A baya dai, gwamnan ya sanar da shiga makarantar koyon haɗa takalma domin nuna wa yan Najeriya muhimmancin hakan
- Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su rinka siyan kayan da aka yi su a ƙasa domin bunƙasa tattalin arziki
Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia, ya bayyana takalmin da ya haɗa da hannunsa a matsayinsa na ɗalibin makarantar Aba-based Footwear Academy, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC
A wata fira da gwamnan yayi da manema labarai, ya nuna takalmin sandal da ya haɗa dakansa yayin da yake murmushi a fuskarsa.
Gwamna Ikpeazu ya sanar da shiga makarantar koyon haɗa takalman sanyawa a watan Mayun da ya gabata.
Gwamna ya yi kira ga yan Najeriya su yi koyi da shi
Bayan shigarsa makarantar, gwamnan ya yi kira ga yan Najeriya da su ɗauki kayan da ake haɗawa a ƙasa da muhimmanci kuma su rinka amfani da su domin hanya ce ta bunƙasa tattalin arziki.
KARANTA ANAN: Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Hallaka Jariri Dan Wata Uku Tare da Mutane da Dama a Benuwai
Ya bayyana cewa tun sanda ya karɓi ragamar mulkin jihar a 2015, kayan da yake sanyawa da takalmansa duk a Najeriya ake yinsu.
"Tun da na karɓi mulki, kayana da takalman da nake sanyawa a cikin ƙasar mu aka haɗa su," inji Gwamnan.
Hotunan gwamnan ɗauke da takalmin
A wani labarin kuma Barka da Sallah: Shugaba Buhari Ya Gwangwaje Yan Bautar Kasa NYSC da Kyautar Kudi da Shanu a Daura
Shugaba Buhari ya baiwa matasa yan bautar ƙasa dake aiki a Daura kyautar kuɗi, shanu da buhunan shinkafa.
Buhari ya nuna jin daɗinsa da ziyarar barka da sallah da matasan suka kai masa har gida, ya kuma roke su da su zama jakadu nagari.
Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya
Asali: Legit.ng