Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin hana majalisar dokokin jihar Zamfara tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, bayan duba karar da Ogwu James Onoja ya shigar a madadin jam’iyyar PDP.

A wani bangare na umarnin, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya kuma sake gargadi gwamnan jihar Zamfara da babban alkalin jihar kan ci gaba da shari’a dangane da duk wani shirin tsige Mahdi Gusau.

Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Onoja ya fadawa kotu cewa majalisar dokoki da wasu na shirin tsige mataimakin gwamnan, saboda kin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Lauyoyin sun ce ya zama dole ga kotu ta shiga tsakani game da batun ta hanyar bayar da dakatarwar wucin gadi ga wadanda ke shirin tsige shi.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a hukuncin da alkalin ya yanke ya ce ya gamsu da cewa lamari ne mai bukatar matukar gaggawa dake bukatar stoma bakin kotu.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Sannan ya umarci bangarorin da su ci gaba da kasancewa yadda suke har zuwa lokacin da za a saurari karar da mai shigar da kara ya shigar.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel