Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin wanke bandaki a Abuja na tsawon kwanaki 60 kan yunkurin damfara
- Wata kotu a Abuja ta yankewa Innocent Destiny hukuncin wanke bandaki a filin wasan Mpape da ke Abuja na tsawon kwanaki 60
- An yi zargin cewa Destiny ya yi kokarin yaudarar wasu mutane a dandalin wechat sannan kuma daga baya aka kama shi
- Kotun ta yanke masa hukuncin wanke bandaki ne bisa la’akari da shekarunsa, da kuma kasancewar karo na farko kenan da ya aikata laifin
Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa wani Innocent Destiny hukuncin wanke bandaki a filin wasa na Mpape da ke Abuja har tsawon kwanaki 60 saboda kokarin yaudarar abokan harka a dandalin isar da sako da ake kira WeChat.
Mai shari’a Kezziah Ogbonnaya ce ta zartar da hukuncin a ranar Litinin, inda ta bayyana cewa yanke irin wannan hukuncin zai taimaka wajen rage cunkoson kotuna, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Nasrun minallah: Dakarun soji sun bindige 'yan Boko Haram 3, sun cafke 11 Borno
An gurfanar da Destiny a gaban kotu saboda nuna kansa a matsayin mace mai suna Kim Webber. Yayin da yake hakan, an zarge shi da yaudarar maza masu amfani da dandalin domin ya damfari su kudade.
Lauyan Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ijeabalum Diribe, ya yi iƙirarin cewa aikata hakan ya saba wa sashi na 322 na dokar fanal kot.
Sakamakon haka, Diribe ya roki kotun da ta yanke wa Destiny hukunci bisa ga yarjejeniyar da aka shigar a ranar 22 ga Yuni, wanda ya bayyana cewa idan aka yanke hukunci mai laifin zai shafe wata guda a gidan yari ko kuma ya biya tarar N100,000.
KU KARANTA KUMA: Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa
Sai dai, lauyan wanda ake kara, Holy Nuhu ya roki kotun da ta yi adalci tare da jin kai ganin cewa wanda ake tuhumar matashi ne kuma wannan ne karo na farko da yake aikata laifi.
EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina
A wani labarin kuma, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Kano ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta hanyar intanet a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar Katsina.
Hukumar, a cikin wata sanarwa a shafinta na Facebook, ta ce wadanda ake zargin galibinsu matasa ne da shekarunsu basu wuce 20 ba.
Sakamakon binciken da jaridar The Nation ta gudanar ya nuna cewa galibin daliban jami’a ne da matasa marasa aikin yi.
Asali: Legit.ng