Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

  • Gwamna Badaru ya bukaci Musulmi suyi addu'a domin kawo karshen kallubalen tsaro
  • Badaru ya bayyana hakan ne cikin sakonsa na sallar da hadiminsa ya fitar ranar Litinin a Dutse
  • Badaru ya kuma tunatar da mutanen jiharsa su rika tunamawa da marasa karfi a tsakaninsu musamman lokacin sallah

Gwamnan jihar Jigawa Mohammadu Badaru ya bukaci al'ummar musulmi su yi amfani da damar salla babba (Ed-el-Kabir) domin yin addu'ar kawo karshen kallubalen tsaro da ke adabar kasar, The Guardian ta ruwaito.

Mr Badaru ya yi wannan kirar ne cikin sakonsa na sallah mai dauke da sa hannun babban mataimakinsa na musamman kan jaridu, Ahmad Danyaro, da ya fitar a ranar Litinin a Dutse.

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Ya ce lokacin babban sallar da ya yi dai-dai da lokacin da aka kammala aikin Hajji a kasa mai tsarki babban dama ce ga yan Nigeria su yi addu'a ga Allah domin samun zaman lafiya a kasar.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Badaru ya tabbatarwa mazauna jiharsa cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki domin zama abi kwatance wurin mulki na gari, tattalin arziki, noma da kasuwanci da janyo masu saka hannun a Nigeria.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Zamu cigaba da bawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari goyon baya a kokarinta na kawo zaman lafiya mai dorewa a kasa.
"Za mu cigaba da daukan matakan da suka sace domin inganta rayyukan mutanenmu.
"Jinjina da muke samu daga kasashen waje na gida Nigeria zai cigaba da bamu kwarin gwiwar cigaba da yi wa mutane hidima."

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Rahoton na The Guardian ya ce gwamnan ya taya musulmi murna a dukkan Nigeria domin sake ganin wani bikin sallar yana tunatar da su kada su manta da biyayya ga Allah.

Ya kuma shawarce su da su rika taimakawa marasa karfi a tsakaninsu kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

Kara karanta wannan

Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labarin mai kama da wannan, yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mata tsohon shugaban karamar hukumar Kaugama, Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

A cewar The Channels, yan bindigan kimanin su 10 ne suka kutsa gidan tsohon shugaban karamar hukumar na Marke, a Jigawa, misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

Daya daga cikin yaran wacce aka sace, Aliyu Ahmad, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce mutanen a kan babur suka taho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel