Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

  • Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola ya biya wa matafiya fiye da 6,000 kudin jirgi daga Legas zuwa Osogbo
  • Gwamnatin jihar ta Osun ta yi hakan ne domin saukakawa mutanen jihar da ke son zuwa bikin sallah gida amma basu da kudin mota/jirgi
  • Mutane da dama da suka amfana da karamcin gwamnatin sun yaba wa gwamnan suna mai cewa ya kamata wasu gwamnonin suyi koyi

A kalla yan Nigeria 6,000 ne suka shiga jirgin kasa daga jihar Legas zuwa Osogbo kyauta da gwamnatin jihar Osun ta biya wa masu zuwa gida hutun Sallah, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda suka amfana da wannan karamcin sun bayyana farin cikinsu bayan sun isa Osogbo a ranar Lahadi suna ta yabawa gwamnatin.

Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah
Matafiya da gwamnan Osun ya biya wa kudin jirgin kasa zuwa Osogbo. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Gwamnatin jihar ta Osun ta bullo da wannan tsarin ne domin saukakawa matafiya wahalar biyan kudin sufuri musamman a wannan lokacin na shagalin sallah.

Kara karanta wannan

Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Bayan isarsu tashar jirgin kasa ta Nelson Mandela Freedom Park da ke Osogbo, wasu daga cikin fasinjojin da suka yi magana da wakilin Daily Trust sun ce sun ji dadin tafiyar kana suka yi wa Gwamna Adegboyega Oyetola godiya.

Abin da wadanda suka shiga jirgin suka ce

Morufat Alao da Olawuyi Abiola da suka shiga jirgin daga Legas zuwa Osogbo, sun bayyana gamsuwarsu da yanayin tafiyar suna mai cewa hakan ya sa sun fara saka rai cewa za a farfado da sufurin jiragen kasa a Nigeria.

Alao ya ce wannan karamcin ta taimaka wa mutane da dama musamman musulmi da rashin kudi yasa ba za su iya biyan kudin sufuri zuwa garuruwansu su yi sallah tare da yan uwansu ba.

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Kalamanta:

"Na yaba wa gwaman bisa wannan karamcin, hakan ya nuna cewa gwamnati ta damu da batun tsaro da walwalar mutanen da suka amfani da abin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

"Na yi mamakin ganin tsaron da aka tanada yayin hawa jirgin a Legas. Ya kamata wasu jihohin suyi koyi da shi.
"Ina iya tunawa yadda jami'an tsaro suka rika kaiwa da kawowa don tabbatar babu wanda ya tada rikici har aka kai Osogbo."

Kazalika, Olawale Abdul-Maleek, Oseni Biyawo, Oyedele, Abdul-Kodir, Usman Abdul-Azeez da Rashidat Owolabi duk sun yabawa matakan tsaron da aka tanada yayin tafiyar zuwa Osogbo.

A bangarensa, kwamishinan Kasuwanci da Masa'antu da Tallafawa Mutane, Dr Bode Olanipekun ya ce Gwamna Oyetola yana tunanin bunkasa irin wannan karamcin domin mutane da dama su amfana.

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Gwamnatin Sokoto ta gwangwaje marayu da makudan miliyoyi

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel