Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

  • Jami'an 'yan sandan Katsina da na Jigawa sun sheke shugaban shahararren 'yan bindiga Abdullahi Bummi
  • A samamen da suka kai maboyarsu a Jigawa, jami'an sun yi nasarar ceto wata tsohuwa mai shekaru 65 a duniya
  • An saci tsohuwar ne daga kauyen Rijiyar Tsamiya dake karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina

Jami'an hukumar 'yan sanda sun sheke shugaban wata kungiyar garkuwa da mutane mai suna Abdullahi Bummi a jihar Jigawa.

An kashe dan ta'addan ne yayin wani samamen da aka kai sansanin 'yan bindigan dake Gallu, karamar hukumar Yankwashi ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an 'yan sanda sun ceto wata tsohuwa mai shekaru 65 yayin samamen wanda aka yi shi na hadin guiwa tsakanin 'yan sandan Katsina da na Jigawa.

KU KARANTA: Lagos: 'Yan kasuwa 3 sun sheka barzahu bayan arangama da sojin sama

Tijjani Ibrahim ya sheke shugaban 'yan bindiga, ya ceto tsohuwa mai shekaru 65
Tijjani Ibrahim ya sheke shugaban 'yan bindiga, ya ceto tsohuwa mai shekaru 65. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Majalisar jihar Kano ta dakatar da bincikar Muhuyi Rimingado

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah yayin jawabi ga manema labarai a hedkwatar hukumar a Katsina, ya ce wacce aka ceto mai suna Hajiya Hasana Zubairu an saceta ne daga kauyensu mai suna Rijiyar Tsamiya dake karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina.

Ya ce masu garkuwan da mutanen sun bukaci kudin fansa har naira miliyan dari biyar daga 'yan uwanta.

"A lokacin da muka samu rahoton saceta, shugaban bangaren yaki da masu garkuwa da mutane tare da hadin guiwar abokan aikinmu na Jigawa sun gaggauta daukar mataki," yace.

Ya ce shugaban 'yan bindigan mai suna Abdullahi Bummi mai shekaru hamsin a duniya ya fara sakarwa 'yan sanda ruwan harsasai yayin da yayi kokarin tserewa da matar a babur amma sai 'yan sanda suka ci karfinsa.

Isah yace masu bincike sun fada dajin da nufin cafko sauran mambobin kungiyar, Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin iyalan matar mai suna Alhaji Rabiu Zubairu yace sun tara kudi har N2.7 miliyan zasu baiwa masu garkuwa da mutanen amma sai suka ce ba zasu karba hakan ba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Jigawa

A wani labari na daban, 'yan gida daya har mutum uku sun rasu a jihar Kwara bayan sun ci guba. An gano cewa sun rasa rayukansu ne sakamakon cin Amala da suka yi a karamar hukumar Ilorin ta gabas.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan uwa biyar ne suka ci abincin. Tuni aka kwashesu zuwa asibuti dake Igboro inda aka tabbatar da mutuwar uku daga ciki.

Wannan na zuwa ne bayan kusan wata daya da irin hatsarin cin guba ya auku a yankunan Baruteen da Kaiama dake karamar hukumar Kwara ta arewa. Rayuka 17 ne suka salwanta sakamakon hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng