Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

  • Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya yi kira ga shugaban kasa da ya kawo rangwame ga talakawansa
  • Sarkin Kanon ya roki shugaba Buhari da ya kawo sassauci a fannin tsaro da kuma hauhawar farashin kaya
  • Shugaba Buhari ya mika godiya tare da cewa ya ji dadin abinda ya gani a jihar Kano na ayyukan gyara rayuwa

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rangwantawa talakawa.

Basaraken yayi wannan kiran bayan karbar bakuncin shugaban kasan a fadarsa a ranar Alhamis.

Ya yi kira ga shugaban kasan da ya inganta tsaro tare da shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna godiya ga shugaban kasa kan wannan ziyarar kuma hakan zai kara dankon alakarsa da gidan sarauta. Gidansa ne dama can. Ba za mu iya fadin sau nawa ya zo gidan ba ballantana a zamanin marigayin Sarki, a yayin shagali da babu," yace.

KU KARANTA: N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari
Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Zamfara: Luguden bama-baman NAF ya aika mata da 'ya'yanta 4 barzahu a Sububu

"Muna fatan mukarrabansa zasu cigaba da yin abinda ya dace ballantana a inda kunnensa baya kaiwa. Muna fatan kammala wannan aikin da aka saka harsashin shi nan babu dadewa.

"Muna kira ga shugaban kasa da ya rangwanta tare da mayar da rayuwa mai sauki ga talakawa ballantana a fannin tsaro da tsaron abinci," ya kara da cewa.

Daily Trust ta ruwaito, a bangarensa, shugaban kasa yace ziyarar ta zama dole saboda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi abinda ya dace da kudin jihar kuma yana son jama'arsa su gani.

"Ina farin ciki da wannan ayyukan. Wadannan ayyukan ya gajesu ne amma saboda na jama'a ne, ya kammala su kuma ya kara da nashi," shugaban kasan yace.

"Na ji cewa ba zan iya zuwa Kano ba tare da na kawo gaisuwa ga mai Martaba ba. Ina farin ciki da abinda nake gani. Nagode sosai," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, 'yan kasuwa uku ne aka gano sun rasa rayukansu sakamakon arangamar da ta auku tsakaninsu da jami'an rundunar sojin sama da 'yan daba a Legas.

Har ila yau, Daily Trust ta ruwaito cewa wasu jama'a da dama sun samu miyagun raunika a fito na fito da aka yi a fitacciyar kasuwa Ladipo dake Mushin, Legas a ranar Talata.

Rikicin ya tirsasa 'yan kasuwa a kasuwar rufe kasuwancinsu domin gujewa abinda zai kai ya kawo. Har yanzu ba za a ce ga dalilin da ya kawo rigimar ba a yayin rubuta wannan rahoton, Daily Trust ta wallafa hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel