Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP

  • Gwamnonin PDPn sun yi zargin cewa razanar da Gwamnonin da suka sauya sheka zuwa APC aka yi
  • Sun ce ba su amince da yanayin mulkin gwamnatin APC ba
  • Sai dai Jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin na Gwamnonin PDP

A jiya ne Gwamnonin Jam’iyyar PDP a Arewa suka yi zargin cewa Gwamnatin Muhammadu tana razanar da su da sauran mambobin jam’iyyar adawa domin su shiga Jam’iyyar APC.

Sun yi ikirarin cewa wadansu takwarorin nasu, ciki har da Ben Ayade Gwamnan Jihar Kuros Riba da Bello Matawalle Gwamnan Jihar Zamfara, wasan a kwanan baya suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki sun yi hakan ba da son ransu ba.

Gwamnonin PDPn sun kuma zargi Gwamnatin Buhari da yi wa Arewa kwange duk kuwa da cewa ita ce iko a siyasance, TheNation ta ruwaito.

Sai dai Jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin da gwamnonin PDP suka yi, inda ta ce nasarorinta suka haifar mata da hakan.

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP
Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP Hoto: Official PDP
Asali: Facebook

KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

Da yake yi wa ’yan jarida bayani bayan taron da ya gudana a gidan Gwamnan Jihar Taraba, a Asokoro, da ke Abuja, Gwamna Darius Ishiaku ya bayyana matakin a matsayin “rashin bin tsarin dimokoradiyya kuma ba abin abin lamuncewa ba. ”

Ya ce:

“Dukkanin gwamnonin PDP da suka koma jam’iyya mai mulki ta APC a ‘yan kwanakin nan sun yi hakan ne saboda tsoratarwa."
"Yawancin membobinmu har yanzu ana tsoratar da su. Muna so a daina razana mu saboda ba mu da natsuwa da hakan. ”

Ya kara da cewa gwamnonin PDP a Arewa ba su gamsu da irin shugabancin da APC ke yi kuma sun yanke shawara su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar hamayyar domin ceto jihohinsu.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Ya ce:

“Dukkanmu mun yanke shawarar cewa gwamnatin APC ba ta samar da shugabancin da ake bukata a Arewa ba. Don haka, mu gwamnonin PDP a Arewa ba mu gamsu da shugabancin gwamnatin APC a Arewa ba.
”Kuma muna jawo hankali cewa duk da cewa shugabanci yana Arewa, ana yi wa yankin kwange. Muna so a lura da hakan.
"Mu kuma gwamnonin PDP mun yanke shawarar cewa, a kashin kanmu mu ci gaba da yin iyakar kokarinmu ga jama’armu kamar yadda muke yi a jihohinmu daban-daban."

Gwamnonin PDP na Arewa duk sun hallara

Sauran gwamnonin PDP na Arewa da suka halarci taron sune Samuel Ortom na Jihar Benue da Aminu Tanbuwal na Jihar Sokoto da Bala Muhammed na Jihar Bauchi da Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa.

APC ta bayyana zargin da gwamnonin suka yi a matsayin "abin dariya."

Sakataren riko na APC na kasa John Akpanudoedehe ya ce nasarorin da Buhari ya samu su ne "wurin jawo hankalin masu shiga jam’iyyar ba tsoratarwa ba."

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya kafa wa PDP hujja da shari'ar Atiku bayan ta fara shirin tsige Matawalle a kotu

Akpanudoehede ya ce: “Wannan zargin da gwamnonin PDP suka yi abin dariya ne. Babu wanda ke tsoratar da kowa ya shiga APC. Mutane suna zuwa bisa radin kansu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel