Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje bisa ayyukan da yake yi a jihar
  • Shugaban kasar ya ce Kano za ta iya gogayya da sauran biranen duniya saboda jajircewa irin na Gwamna Ganduje
  • Shugaba Buhari ya yabawa Ganduje bisa karasa ayyukan da gwamnatocin da suka gabace shi suka fara yana mai cewa hakan zai habaka jihar da kasa baki daya

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya ce jihar Kano za ta iya gogayya da takwarorinta a duniya saboda jajircewa irin na gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, The Punch ta ruwaito.

Ya umurci gwamnonin jihohi su rika koyi da al'adar cigaba daga inda magabantansu suka tsaya domin ciyar da jihohinsu da kasa gaba.

Kano Za Ta Iya Goggaya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A cewar The Punch, Buhari ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, jim kadan bayan kaddamar da aikin shimfida layin dogo na Kano zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya yabi Ganduje, ya ce Gwamnan Kano ba mugu ba ne

Ya ce:

"Na zo Kano ne domin ganin wasu ayyuka da gwamnati mai ci yanzu karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi, na yi farin ciki da abin da na gani. Gwamnan yana kokarin ganin cewa ba a bar jihar a baya ba.
"Kano za ta iya gogayya da wasu jihohin a duniya, saboda irin jajircewa na gwamnan, wanda ya dage wurin karasa ayyukan da gwamnatocin da suka gabace shi suka fara."

KU KARANTA: 'Karfin Hali: Ƴan Bindiga Sun Fara Rubutawa Mutane Wasika Kafin Su Kawo Hari a Sokoto

Shugaban kasar ya jadada niyyar gwamnatinsa wurin bulla da shirye-shirye da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yan Nigeria.

Tunda farko, Gwamna Ganduje ya ce mayar da hankali da gwamnatin tarayya ta yi wurin farfado da sufuri a kasar alama ce da ke nuna cewa tattalin arzikin Nigeria zai sake bunkasa.

Ya yi bayanin cewa annobar coronavirus ta shafi tattalin arzikin kasashen duniya baki daya.

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Ganduje ya ce:

"Na yi farin ciki game da aikin layin dogo na Kano zuwa Kaduna wadda zai habbaka tattalin arziki da farfado da bangaren sufuri."

Shugaban kasa Buhari ya yabi Ganduje, ya ce Gwamnan Kano ba mugu ba ne

A wani rahoton daban Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabi gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ya ziyaci jihar Kano a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, 2021.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnan na Kano ba mugun shugaba ba ne.

Shugaban Najeriyan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a fadar sa bayan kaddamar da aikin jirgi..

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel