Cikakken jerin sunayen 'yan takarar da INEC ta tantance domin zaben gwamna
Gabanin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba a jihar Anambara, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen wadanda aka tabbatar da ingancinsu a zaben.
Duba ga takardar da aka buga a shafin yanar gizon INEC, Legit.ng ta lura cewa ba a ambaci kowani dan takara ba a Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Hukumar ta bar bangaren jam'iyyar babu komai sannan ta sanya "umarnin kotu" a bangaren tsokaci.
KU KARANTA KUMA: 2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu
Hakazalika, babu sunan Farfesa Chukwuma Soludo, dan takarar jam'iyyar APGA, a cikin jerin sunayen. Maimakon haka, hukumar zaben ta kasa ta sanya sunan wani dan takarar jam’iyyar APGA, Chukwuma Michael Umeoji, inda ta yi nuni ga umarnin kotu.
KU KARANTA KUMA: Dokar Zabe: Ƴan Majalisar PDP Sun Harzuka, Sun Fice Daga Zauren Majalisa a Fusace
Ga cikakken sunayen a kasa:
1. Ekene Alex Nwankwo (Accord Party, A)
2. Doreen Ifeoma Madukaarisa (Action Alliance, AA)
3. Obi Sylvester Chukwudozie (African Action Congress, AAC)
4. Akachukwu Sullivan Nwankpo (African Democratic Congress, ADC)
5. Prince Ume-Ezeoke Afam Luke Douglas (Action Democratic Party, ADP)
6. Emmanuel Andy Nnamdi Uba (All Progressives Congress, APC)
7. Chukwuma Michael Umeoji (All Progressives Grand Alliance, APGA)
8. Eze Robinson Chukwuma (Allied Peoples Movement, APM)
9. Azubuike Philip Echetebu (Action Peoples Party, APP)
10. Chika Jerry Okeke (Boot Party, BP)
11. Agbasimalo Obiora Emmanuel (Labour Party, LP)
12. Ohajimkpo Leonard Emeka (New Nigeria Peoples Party, NNPP)
13. Adaobi Uchenna Okpeke (National Rescue Movement, NRM)
14. Nnamdi Nwawuo (Peoples Redemption Party, PRP)
15. Ekelem Edward Arinze (Social Democratic Party, SDP)
16. Ifeanyi Patrick Ubah (Young Progressive Party, YPP)
17. Ugwoji Martin Uchenna (Zenith Labour Party, ZLP)
Babu sunan PDP yayin da INEC ta saki jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Anambra
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da Jam’iyyar PDP a cikin jerin ‘yan takarar da aka tantance don zaben gwamnan Anambra na ranar 6 ga Nuwamba.
Hukumar a cikin wata sanarwa daga Kwamishinanta na Kasa kuma Shugaban kwamitin yada labarai da kuma wayar da kan Masu Zabe, Festus Okoye, ya bayyana umarnin Kotu na cire sunan dan takarar jam’iyyar daga jerin sunayen da aka tantance, jaridar The Nation ta ruwaito.
Har ila yau an rasa sunan dan takarar bangaren aware na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) Farfesa Chukwuma Soludo.
Asali: Legit.ng