Da dumi-dumi: Babu sunan PDP yayin da INEC ta saki jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Anambra

Da dumi-dumi: Babu sunan PDP yayin da INEC ta saki jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Anambra

  • Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta cire sunan dan takarar Jam’iyyar PDP a cikin jerin ‘yan takarar da aka tantance don zaben gwamnan Anambra.
  • INEC ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan umarnin Kotu da ta samu na cire sunan dan takarar jam’iyyar daga jerin sunayen da aka tantance.
  • Za a gudanar da zaben gwamnan jihar ne a ranar 6 ga Nuwamba.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi watsi da Jam’iyyar PDP a cikin jerin ‘yan takarar da aka tantance don zaben gwamnan Anambra na ranar 6 ga Nuwamba.

Hukumar a cikin wata sanarwa daga Kwamishinanta na Kasa kuma Shugaban kwamitin yada labarai da kuma wayar da kan Masu Zabe, Festus Okoye, ya bayyana umarnin Kotu na cire sunan dan takarar jam’iyyar daga jerin sunayen da aka tantance, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya caccaki majalisar dattawa, ya ce mika ikon INEC ga NCC ya saba wa kundin tsarin mulki

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

Da dumi-dumi: Babu sunan PDP yayin da INEC ta saki jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Anambra
Babu sunan PDP yayin da INEC ta saki jerin ‘yan takarar zaben gwamnan Anambra Hoto: Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Har ila yau an rasa sunan dan takarar bangaren aware na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) Farfesa Chukwuma Soludo.

Sai dai Hukumar ta tantance dan takarar daya bangaren na APGA Chukwuma Micheal Umeoji don zaben, inda Soludo, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fada halin rashin tabbass.

A wani labarin na daban, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, ta nada Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba a matsayin sabon mataimakin bulaliyar majalisar dattawa.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar nadin Danbaba a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, a zauren majalisar.

Wasikar da aka ambata tana dauke da sanya hannun sakataren jam'iyyar adawa ta kasa, Ibrahim Tsuari, jaridar The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng