Da dumi-dumi: PDP ta nada sabon mataimakin bulaliyar majalisar dattawa
- Sauya sheka da Sanata Sahabi Ya'u ya yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress a Zamfara ya sanya PDP ta yi sabon nadi
- Jam’iyyar adawar a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, ta zabi sabon mataimakin bulaliyar majalisar dattawan Najeriya
- Sabon wanda aka nada shi ne Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba wanda ke wakiltar yankin Sokoto ta Kudu
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, ta nada Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba a matsayin sabon mataimakin bulaliyar majalisar dattawa.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar nadin Danbaba a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, a zauren majalisar.
KU KARANTA KUMA: Jama’a sun fusata yayin da gwamnatin jihar Taraba ta fara siyar da fom din daukar aiki

Asali: Facebook
Wasikar da aka ambata tana dauke da sanya hannun sakataren jam'iyyar adawa ta kasa, Ibrahim Tsuari, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Ta’addanci: Mataimakin gwamnan Zamfara ya shiga gagarumin matsala bayan gangamin PDP
Sabon wanda aka nada, mai wakiltar yankin Sokoto ta Kudu a majalisar dattawa, ya cike mukamin magabacinsa, Sanata Sahabi Ya’u, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
KU KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano
Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna
A wani labari na daban, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce tana nan kan matsayinta na cewa sai an rantsar da mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau a matsayin gwamnan jihar.
A cewar jam'iyyar adawar, gwamna Bello Matawalle ya rasa damar zama a kujerar a daidai lokacin da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Daily Nigerian ta ruwaito.
Legit.ng ta tattaro cewa PDP ta sake jaddada matsayinta game da rikicin na Zamfara a cikin wata sanarwa daga kakakinta, Kola Ologbondiyan.

Kara karanta wannan
Matawalle: PDP ta ce lallai sai an rantsar da mataimakin gwamnan Zamfara a matsayin gwamna
Asali: Legit.ng