Dokar Zabe: Ƴan Majalisar PDP Sun Harzuka, Sun Fice Daga Zauren Majalisa a Fusace

Dokar Zabe: Ƴan Majalisar PDP Sun Harzuka, Sun Fice Daga Zauren Majalisa a Fusace

  • Wasu yan majalisar dokokin tarayya na PDP sun fice daga zauren majalisar cikin fushi a ranar Juma'a
  • Yan majalisar na PDP sun fusata ne saboda masu rinjaye sun ki amincewa a bawa INEC karfin ikon aika sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo
  • Wannan gyaran da aka so yi wa dokar zaben ya shafi kashi 25 karamin kashi na 3 ne a turance 'Clause 52'

Wasu daga cikin yan majalisar wakilai na tarayya yan jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) sun fice daga zauren majalisa kan batun yi wa dokar zabe garambawul ta 'Clause 52', Daily Trust ta ruwaito.

Kudirin dokar ya janyo cece-kuce a majalisar wakilai ta tarayya da majalisar dattawa a ranar Alhamis 15 ga watan Yulin shekarar 2021.

Ya majalisar marasa rinjaye na son a bawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC damar aika sakamakon zabe ne ta hanyar yanar gizo amma hukumar sadarwa ta NCC ta ce bata da isasun kayan aiki.

Kara karanta wannan

Majalisar tattalin arziki ta na shirin amincewa a kara farashin fetur a gidajen mai daga N165

Dokar Zabe: Ƴan Majalisar PDP Sun Harzuka, Sun Fice Daga Zauren Majalisa a Fusace
Majalisar Wakilai na Tarayyar Nigeria. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yan majalisar wakilan na PDP suna ganin rashin tura aika sakamakon zaben ta yanar gizo zai iya bada kafar a rika tafka magudi yayin zaben.

DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Amma, duk da cewa majalisar dattawa ta amince da kundin dokar a ranar Alhamis, ba a amince da shi a majalisar wakilan ba.

Shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu, shine ya jagoranci yan majalisar na jam'iyyar PDP suka fice daga zauren majalisar a ranar Alhamis da rana.

Elumelu, ya nuna rashin yardarsa da amincewar da 'Clause 52' tare da wasu sassan dokokin duk da cewa ba a cimma matsaya a kansa ba.

Ya bayyana cewa yan majalisar jam'iyyar hamayya ba za su zuba ido suna kallo a ki kulawa da damuwarsu ba.

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Kara karanta wannan

Sanatocin APC sun ki amincewa da tura sakamakon zabe ta na'ura

Sai dai majalisar ta amince da kudirin dokar zaben da aka yi wa garambawul duk da ficewar da marasa rinjayen suka yi saboda kin amincewar shugaban zaman, Ahmed Idris Wade, ya sake sauraron kudirin domin bada damar tura sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo, This Day ta ruwaito.

Yan majalisar marasa rinjaye daga bisani sun shaidawa manema labarai cewa mataimakin kakakin majalisar ya basu kunya, da kuma hukumar Kula da Sadarwa ta kasa NCC, da suka yi karyar cewa ba su da isasun kayan aikin da za su tura sakamakon zabe ta yanar gizo.

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsageru Sun Kai Hari Banki, Sun Sheke Dan Jarida da Wasu Mutum 2

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel