Da dumi-dumi: Rikici ya barke a zauren majalisa kan batun masana'antar man fetur

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a zauren majalisa kan batun masana'antar man fetur

Rikici ya barke a zauren majalisar wakilai a ranar Alhamis kan Dokar Masana’antar Man Fetur (PIB), Daily Trust ta ruwaito.

Rikicin ya fara ne bayan da wasu ‘yan majalisar suka tada jiyoyin wuya kan zargin ragin kaso da aka amince akai ga al’ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur.

Majalisar ta riga ta zabi 5% ga al'ummomin dake zaune a yankuna masu man fetur a cikin kudurin PIB a baya yayin da Majalisar Dattawa ta zartar da 3%.

Da dumi-dumi: Rikici ya barke a zauren majalisa kan batun masana'antar man fetur
Zauren majalisa | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai, wani dan majalisar wakilai na PDP, Chinyere Igwe, ya kirkiro wani yanayi ta hanyar ihu da babbar murya kan zargin ragin kaso ga al'ummomin daga 5% zuwa 3% bayan kwamitin taron na duka majalisar dattijai da ta Wakilan sun daidaita akan kashi 5%.

Kafin shigowar Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, dan majalisar ya yi ruri da cewa:

"Dole ne ya zama 5%."

Ko da Shugaban majalisar ya iso zauren majalisar ya hau kujerarsa, rikicin na ci gaba da takaddama lamarin da ya tilasta Shugaban Majalisar ya nemi Majalisar da ta tafi zaman zartarwa.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

A yanzu haka ‘yan majalisar suna cikin taron zartarwa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel