Majalisar tattalin arziki ta na shirin amincewa a kara farashin fetur a gidajen mai daga N165

Majalisar tattalin arziki ta na shirin amincewa a kara farashin fetur a gidajen mai daga N165

  • Majalisar NEC ta yi taron da ta saba a karkashin Mataimakin Shugaban kasa
  • Yemi Osinbajo ne ya ke jagorantar zaman Majalisar tattalin arzikin Najeriya
  • Kwamiti ya ba Majalisar shawara game da tsaida farashin fetur, tallafin mai

Majalisar da ke kula da tattalin arzikin Najeriya, NEC, ta zauna a ranar Alhamis, 14 ga watan Yuli, 2021, inda ta tattauna a kan sha’anin man fetur da NNPC.

Daily Trust ta ce majalisar ta zauna ne a kan abubuwan da ke faru wa da kamfanin mai na NNPC, da yadda gwamnati za ta cire hannunta daga harkar fetur.

Haka zalika wannan majalisa ta tabo abin da ya shafi farashin litar man fetur a Najeriya a zaman.

KU KARANTA: Ba za a kara kudin mai ba - Gwamnati

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne shugaban wannan majalisa. Hadiminsa, Laolu Akande, ya fitar da jawabi bayan an kammala taron.

Laolu Akande yace majalisar NEC ta dauki shawarwari da bayanan da aka kawo wajen wannan zama da aka yi jiya, ya ce za su duba abubuwan da aka kawo.

Kara karanta wannan

Ana so ayi amfani da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a karya tattalin Arewa – Kungiya

A cewar Akande, nan gaba za a fitar da cikakken rahoton bukatun da kwamiti ya gabatar wa NEC.

Mai magana da yawun bakin mai girma mataimakin shugaban Najeriyan, ya ce majalisar ta duba kokarin da ake yi wajen maida motoci su koma aiki da gas.

KU KARANTA: Za ayi yajin-aiki idan aka kara kudin fetur inji NLC

Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo a taron NEC Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wani kwamiti na musamman da aka kafa a kan batun harkar mai ya gabatar da shawarwarinsa, wanda daga ciki akwai maganar gwamnati ta kara farashi a kasar.

Majalisar ta NEC ta kuma karbi rahoto game da tallafin da gwamnatin tarayya ke ba gwamnonin jihohi domin aiwatar da ayyukan da suka sa a cikin kasafin kudinsu.

Ganin cewa sallar idi ta gabato, majalisar ta bada shawarar a dage wajen bin matakan yaki da cutar COVID-19 kamar yadda hukumar NCDC ta gindaya sharudodi.

Yadda aka dauko abin

Idan za ku tuna a kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti da zai duba lamarin cire tallafin mai.

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: Majalisa ta amince da rokon cin danyen bashin Naira Tiriliyan 4

Wannan kwamitin da ke karkashin Nasir El-Rufai bada shawaran cewa a cire tallafin fetur, sannan a kara farashin lita ya zama tsakanin N380 zuwa sama da N400.

Asali: Legit.ng

Online view pixel