Da Ɗumi-Dumi: An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu

Da Ɗumi-Dumi: An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu

  • Yan bindiga sun kaiwa ɗaliban jami'ar jihar Delta hari yayin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta
  • Maharan sun kashe ɗalibi ɗaya, Odje Stephen, sannan suka yi awon gaba da wasu guda biyu, Jennifer da Divine
  • Ƙungiyar ɗaliban jami'ar DELSU ta maida martani kan lamarin, inda ta bayyana ɗaliban jami'ar a matsayin abin harin yan bindiga

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kashe wani ɗalibin jami'ar jihar Delta (DELSU), Odje Stephen, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa makaranta, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

A cewar wata majiya, bayan kashe Stephen a harin da aka kai ƙauyen Oria da yake ɗaukar ƙasa da mintuna 15 zuwa DELSU, yan bindigan sun yi awon gaba da Mr. Divine Omajuwa, da Miss Hamza Hussiena Jennifer, a kan hanyarsu ta komawa makaranta.

Kara karanta wannan

Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Rahoton thisday ya bayyana cewa, har yanzun ba'a gano dalilin da yasa maharan suka kashe Stephen ba kuma suka sace ɗalibai guda biyu.

Jami'ar jihar Delta, DELSU
Da Ɗumi-Dumi: An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Hoto: schoolings.org
Asali: UGC

DELSU ta yi martani kan harin

Da take martani kan faruwar lamarin, hukumar jami'ar DELSU, ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ɗalibinta Stephen da kuma sace Jennifer da Divine.

A wani jawabi da jami'ar ta fitar ɗauke da sa hannun mai kula da al'amuran ɗalibai, Farfesa Chukwujindu Iwegbue, ta yi kira ga "Dukkan hukumonin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da an kuɓutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya."

Jawabin ya ƙara da cewa duk waɗanda suke da hannu kan kai hari ga ɗalibai da ba ruwansu, ya kamata a cafko su, a hukunta su.

Hakanan, jami'ar ta yi ta'aziyya ga iyalan ɗalibin da ya rasa ranshi a yayin harin.

Jami'an tsaro ba su taɓuka komai idan haka ta faru

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari Baki Ɗaya Saboda Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Ƙungiyar ɗalibai ta jami'ar SUG-DELSU, ta bayyana cewa a halin yanzun ɗaliban jami'ar sun zama abin hari, kisa da kuma garkuwa da su ga yan bindigan da suka shigo jihar.

A wani jawabi da shugaban SUG, Mukolo Ogelenya, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa irin wannan harin zai iya jawo rashin bin doka a garin Abraka dama jihar baki ɗaya matuƙar ba'a ɗauki matakin da ya dace ba.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Yace: "Babban abun takaicin shine idan irin haka ta faru, hukumomin tsaro basa yin komai don hukunta masu aikata haka."

Shugaban ɗaliban ya miƙa ta'aziyyarsa a madadin ɗaliban Jami’ar baki ɗaya ga iyalan wanda ya rasa rayuwarsa.

A wani labarin kuma Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi ikirarin ba zai taba komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC ba.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Gwamnan yace jam'iyyar PDP kaɗai zata iya warware matsalolin da gwamnatin APC ta jefa Najeriya a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel