IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

  • Kungiyar masu fafutikar kafa Biafra, IPOB, ta ce gwamnonin Nigeria biyu da minista da dan kasuwa ne suka dauki nauyin kamo Nnamdi Kanu
  • Kungiyar ta lissafa sunayen Gwamnan Rivers Nyesome Wike da Willie Obiano na jihar Anambra da Ministan Kwadago Chris Ngige da dan kasuwa Emeka Offor
  • IPOB ta gargadi mutanen da ta lissafa cewa su tabbata sun fito da Kanu daga hannun gwamnatin Nigeria idan ba haka ba za su gane kurensu

Haramtaciyar kungiyar masu son kafa kasar Biafra, IPOB, ta ce Gwamnan Rivers Nyesome Wike da takwararsa Willie Obiano na jihar Anambra ne suka bada kudade domin a kamo shugabanta, Nnamdi Kanu, SaharaReporters ta ruwaito.

A cewar sanarwar da kakakin IPOB, Emma Powerful, ya aike wa SaharaReporters a ranar Alhamis, gwamnonin biyu ne suka bawa gwamnatin Nigeria gudunmawa domin kamo shugaban masu son ballewa daga kasa domin wasu dalilai nasu na siyasa.

Kara karanta wannan

Shirin Sallah: Wani gwamna ya biya ma'aikata albashi, ya rabawa gajiyayyu kudade

IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: NewsWireNG
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Sanarwar ta kara da cewa Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Dr Chris Ngige da dan kasuwa Cif Emeka Offor suma sun taka rawa wurin jefa Kanu cikin halin da ya shiga a yanzu.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Kungiyar IPOB karkashin jagorancin jarumin shugaban mu, Mazi Nnamdi Kanu, ta gano wadanda suka ci amanar shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu suka mika shi hannan azzalumar gwamnatin Nigeria ta Fulani ta hanyar hadin gwiwa da gwamnatin Kenya.
"Sashin bincikenmu na sirri, M.Branch ya gano yadda Emeka Offor na Oraifte ya shirya abin kuma ya dauki nauyi. Mun gano da farko gwamnatin Nigeria bata amince ba har sai da Emeka Offor, Nyesome Wike da Willie Obiano suka amince za su dauki nauyin biyan kudaden da za a kashe wurin shirya abin."

Kara karanta wannan

Hatsarin motocci ya yi sanadin salwantar rayyuka 9 a Yobe

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Sanarwar ta kuma yi ikirarin cewa Offor yana shirin kafa wata gidan Rediyo na Biafra da kudi Naira miliyan 250 wacce za ta rika adawa da shirin Kanu na ballewa daga Biafra.

"Idan wani abu ya samu shugabanmu Mazi Nnamdi Kanu, hukuncin da zai fada kan wadanda suka ci amanarsa zai fi wanda ta samu Judas. Duk wanda ke kusa da su ya shawarcesu su tabbatar gwamnatin Nigeria ta sako shi."

Kungiyar ta ce za ta cigaba da bincike domin gano iya abin da kowannen cikinsu ya aikata.

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel