Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

  • Sanatoci zasu gyara wasu dokokin hukumar JAMB domin inganta ɓangaren ilimi a Najeriya
  • Kwamitin ilimi na majalisar dattijai ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai hukumar JAMB
  • Sanata Akan Eyakenyi, tace shekaru na da matuƙar muhimmanci a karatu, kuma zasu ƙayyade adadin shekarun rubuta UTME

Kwamitin ilimi na majalisar dattijan Najeriya, a ranar Talata, ya bayyana cewa zai yi garambawul a wasu dokokin hukumar JAMB, domin maida shekara 16 mafi ƙarancin shekarun ɗalibin da zai zauna jarabawar share fagen shiga manyan makarantu UTME.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Kwamitin ya ƙara da cewa duk wani ɗalibi da bai kai shekara 16 ba, bai kamata a bashi gurbin shiga jami'a ba domin shekaru na taka rawa wajen karatun ɗalibai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Mataimakiyar shugaban kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi, ita ce ta faɗi haka yayin wata ziyara da suka kaiwa hukumar JAMB ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari Baki Ɗaya Saboda Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Majalisar Dattijai
Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanatan tace zasu maida hankali kan wasu wurare biyu wajen gyaran domin inganta hukumar dake shirya jarabawar.

"Idan ba'a shirya ɗaliban makarantar sakandire yadda ya kamata ba kafin a ba su damar shiga jami'a, to tabbas idan suka je zasu samu matsaloli." a cewar sanatan.

Ta bayyana hukumar JAMB a matsayin wani mataki dake tsakanin sakandire da jami'a, kuma ya zama wajibi a gyara hukumar domin samun ingantaccen ilimi a Najeriya.

Eyakenyi ta yaba wa hukumar bisa shirya jarabawar UTME 2021 kuma aka kammala ta lami lafiya, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi

Bamu da hurumin ƙayyade shekarun dalibai

Da yake maida martani, shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya faɗa wa kwamitin cewa hukumar ba ta da hurumin hana ɗalibi rubuta jarabawar a dalilin shekaru.

Ya bayyana cewa makarantu ne suke da alhakin wanene ya cancanta su ɗauka, kamar jami'ar Ibadan da bata bada gurbin karatu ga duk wanda bai kai shekara 16 ba.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

A wani labarin kuma Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi ikirarin ba zai taba komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta APC ba.

Gwamnan yace jam'iyyar PDP kaɗai zata iya warware matsalolin da gwamnatin APC ta jefa Najeriya a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel