Bidiyo ya bayyana yayin da jama'a suka yi tururuwan fitowa don tarbar Shugaba Buhari a Kano
- Fadar shugaban kasa ta wallafa faifan bidiyon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar Kano
- Shugaban kasar ya samu kyakkyawar tarba daga gwamnatin Kano da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje
- Shugaban na Najeriya ya kuma kaddamar da ayyuka a jihar baya ga ziyarar wasu muhimman wurare
Daruruwan mazauna jihar Kano sun yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kyakkyawar tarba yayin ziyarar aiki da ya kai jihar a ranar Alhamis 15 ga watan Yuli.
Buhari Sallau, mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai, ya wallafa bidiyo a shafin Facebook wanda ke nuna mazauna jihar yayin da suke sanya shugaban kasar farin ciki a Kano.
KU KARANTA KUMA: Jama’a sun fusata yayin da gwamnatin jihar Taraba ta fara siyar da fom din daukar aiki
Ya bayyana Kano a matsayin wurin a matsayin ginshikin siyasar Shugaba Buhari.
Buhari ya kaddamar da aiki
Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa a yayin ziyarar tasa, Buhari ya kaddamar da gadar Dangi/karkashin kasa da ke Zoo Road.
Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai na zamani, ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Buhari ya kaddamar da fara ginin layin dogo daga jihar Kano zuwa Kaduna.
Ya bayyana cewa, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a lokacin da yake jawabi a wurin taron ya ce babbar tashar da za a gina a Zawaciki, za ta zama tashar jirgin kasar da ta fi girma a duk Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka
Shugaban kasar ya kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a fadarsa.
Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira garin Zawaciki, inda aka shirya kaddamar da fara ginin layin dogo daga jihar Kano zuwa jihar Kaduna.
Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ya bayyana cewa gwamnoni da Ministoci tuni sun dira garin kuma suna saurarin zuwan shugaban kasan ne.
Za’ayi tashohin jirgin kasa a Kaduna, Jaji, Zaria, Kwakwa, Madobi da Kano.
Asali: Legit.ng