Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin gina jirgin kasan daga Kano-Kaduna da ake ta jira

Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin gina jirgin kasan daga Kano-Kaduna da ake ta jira

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin gina jirgin kasan Kano-Kaduna
  • Gwamnatin Najeriya ta ce wannan jirgin zai taso ne daga Rigasa har zuwa Zawaciki
  • Tashar jirgin da za a gina a garin Zawaciki, za ta fi kowace girma idan an gama aikin

Jaridar This Day ta rahoto cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da aikin gina jirgin kasan Kano-Kaduna mai tsawn kilomita 203.8.

Muhammadu Buhari ya taka kasa a Kano

Kamar yadda mu ka samu labari wajen daya daga cikin hadiman shugaban kasa, Bashir Ahmaad, Muhammadu Buhari ya isa Kano da karfe 12:00 na rana.

Jirgin fadar shugaban kasar ya sauka a garin Zawaciki, karamar hukumar Dawakin Kudu dazu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna

Mai ba shugaban kasar shawara ya ce tawagar Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bayan kaddamar da aikin.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran PDP a Zaben 2023, Ya Cire Gabar Siyasa, Ya Yabi Shugaba Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganin mutanen da su ka tarbi shugaban kasar, hadimin na sa ya ce idan aka ce babu inda Buhari ya kafu a siyasa, ya tara mutane irin Kano, to an yi daidai.

Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa babbar tashar da za a gina a Zawaciki, za ta zama tashar jirgin kasar da ta fi girma a duk Najeriya.

Yadda aikin wannan jirgin kasa zai kasance

Jirgin da za a gina zai fara ne daga Rigasa (Kaduna), ya zo Zawaciki (Kano). Wannan dogo da zai hada jihohin Arewan biyu ya na da tsawon kilomita 203.8

Shugaba Buhari ya kaddamar da jirgi
Jirgin kasa a Kaduna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Masu zuwa Abuja daga Kaduna ta jirgin hadu da ‘Yan bindiga

Idan har gwamnatin tarayya ta iya kammala wannan gagarumin aikin, mutum zai iya zuwa tun daga garin Kano har birnin tarayya Abuja ta jirgin kasa.

Kara karanta wannan

2023: Kar Ku Yi Danasani da Mulkin Buhari, Tinubu Ga Yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce jirgin Abuja-Kaduna mai tafiya a kan kilomita 150 zai hadu da Kano.

Za a samu manya da matsakaitan gadoji 13 a hanyar jirgin. Akwai wasu gadoji 17, tare da manyan titunan sama 60, da gadojin tsallaka titi 12 duk a hanyar,

This Day ta ce za a samu kwalbati 374, tare da tashoshi uku da za su ratsa wannan titin jirgin kasa.

A yau Alhamis ne ‘Yan Majalisar dattawa su ka sake yarda cewa gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya cin bashin kudi daga wasu bankunan kasashen waje.

Najeriya za ta karbo $8,325,526,537.0 da €490, 000, 000 domin ayi ayyukan more rayuwa a jihohi.

Ga bidiyon bikin kaddamawar nan a shafin Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel