Ana so ayi amfani da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a karya tattalin Arewa – Kungiya

Ana so ayi amfani da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a karya tattalin Arewa – Kungiya

  • Kungiyar CNG ta yi Allah-wadai da matakin saida wasu kamfanonin wutar lantarki
  • CNG ta ce ba komai ya sa aka kawo wannan shiri ba sai domin a karya ‘Yan Arewa
  • Abdul-Azeez Suleiman yace ana amfani da Yemi Osinbajo domin a cin ma wannan

Gamayyar kungiyoyin Arewa ta CNG ta ce majalisar Farfesa Yemi Osinbajo da ke kula da tattalin arziki ta na neman nakasa tattalin yankin Arewa.

Kungiyar ta CNG ta zargi ofishin mataimakin shugaban kasa da amfani da damarsa wajen saida wasu murafan wutar lantarki biyar ga ‘yan kasuwa.

CNG ta bukaci Osinbajo wanda shi ne shugaban majalisar tattalin arziki na NEC da NCP mai alhakin saida kadarorin gwamnati, ya sake shawara.

KU KARANTA: Za mu ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci – Osinbajo

Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar ta na so a janye maganar saida murafan wutar lantarki na Calabar, Ihovbor, Olorunsogo, Omotosho da Geregu.

Kara karanta wannan

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

Mai magana da yawun bakin kungiyar CNG, Malam Abdul-Azeez Suleiman, ya fitar da jawabi a Abuja, ya na sukar matakin da majalisun suka dauka.

Abdul-Azeez Suleiman ya zargi Farfesa Osinbajo da rashin tunani da zaluntar mutanen Arewa, ya yi kira ga shugabannin yankin da su farga tun da wuri.

Kamar yadda jaridar ta rahoto a ranar Talata, Suleiman ya ce an dauki wannan mataki ne da nufin kara gurgunta mutanen Arewa da mugun talauci.

Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Jihohin Najeriya 10 da su ka fi sauƙin yin kasuwanci

“CNG lura da sabon shirin da wasu manyan Kudu suke yi, na amfani da matsayin Yemi Osinbajo na shugaban majalisar tattalin arziki da majalisar da ke da alhakin saida kadarorin gwamnati da hukumar BPE, na karya karfin yankin Arewa.”
“Mu na kira ga duka masu ruwa da tsaki a Arewa suyi magana da babbar murya, su kare Arewa daga wannan shiri na wadanda suke ganin dole a bar yankin ya cigaba da zama cikin talauci.”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Kawo yanzu mai girma Farfesa Yemi Osinbajo bai fito ya yi magana a kan wannan zargin ba.

A karshen zaman FEC na jiya, Babatunde Fashola ya bayyana cewa kamfanin Dangote zai gina titunana biyar a kan Naira biliyan 309 domin a yafe masa haraji.

A madadin ya biya gwamnatin tarayya haraji, Dangote zai shimfida tituna a wasu Jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng