Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi

Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi

  • Shugaba Buhari zai kai ziyara jiharsa ta Katsina, inda ake tsammanin zai ƙadɗamar da wasu muhimman ayyuka
  • Shugaban zai ƙaddamar da aikin ruwa na Zube Dam a Dutsinma shekara sama da 40 bayan fara shi
  • Ana sa ran Buhari zai kaddamar da wani aikin hanya mai tsawon kilomita 50 da gwamnatin Masari ta yi

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jiharsa ta Katsina ranar Alhamis, kuma ana tsammanin zai ƙaddamar da aikin ruwa na Zobe Dam da ya laƙume biliyoyin kuɗi da kuma hanyar Dutsinma-Tsaskiya mai kilomita 50, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yan Ta'addan da Luguden Wutar Sojoji Ya Koro Suna Tattaruwa a Yankunan Jihata, Gwamna Ya Koka

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da mai taimakawa gwamnan Katsina kan yaɗa labarai, Abdu Labaran Malumfashi, ya fitar.

Gwamnatin Buhari ta ƙarisa aikin ruwa na Zobe Dam shekara 40 bayan fara shi, yayin da gwamnatin Katsina ta aiwatar da aikin hanyar Dutsinma-Tsaskiya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Shugaba Buhari tare da Gwamna Masari
Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi Hoto: @BashirAhmad
Asali: Instagram

A jamhuriya ta biyu aka fara Zobe Dam

Abdu Labaran, ya bayyana a jawabinsa cewa an fara aikin ruwa na Zobe Dam tun a zamanin mulkin jamhuriya ta biyu na shugaban ƙasa, Shehu Shagari, amma sai yanzun aka ƙarisa shi.

Jawabin yace: "Aikin ruwa na Zobe Dam wanda ya laƙume biliyoyin Nairori, an fara shi ne tun a shekarar 1980 a lokacin mulkin jamhuriya ta biyu na Shugaban ƙasa, Shehu Shagari."

"Amma sai kwanan nan ne gwamnatin Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, na jam'iyyar APC ta kammala shi."

KARANTA ANAN: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

"Hakazalika, aikin hanya mai tsawon kilomita 50 da ta taso daga Dutsinma zuwa Tsaskiya, Gwamnatin APC ce ta fara shi a shekarar 2017 kuma ta kammala ƙarƙashin mulkin Gwamna Aminu Bello Masari."

A wani labarin kuma COVID19: Wata Jami'a Ta Umarci Dalibai Su Koma Gida Har Sai Baba Ta Gani

Kara karanta wannan

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Shugaban PDP na kasa da Gwamna Wike

Jami'ar gwamnatin tarayya dake Lagos (UNILAG) ta umarci ɗalibanta su fice daga ɗakin kwanansu cikin gaggawa.

Hukumar jami'ar ta ɗauki wannan matakin ne a wani taron gaggawa da ta gudanar ranar Laraba saboda ɓarkewar COVID19.

Asali: Legit.ng

Online view pixel