Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Shugaban Kwalejin Fasaha a Zamfara

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Shugaban Kwalejin Fasaha a Zamfara

  • Yan bindiga sun sako shugaban kwalejin fasaha dake Bakura, Mr. Habibu Mainasara, kwana uku bayan sace shi
  • Ɗan uwan shugaban, Nasiru Mainasara, ya tabbatar da cewa an sako shi ranar Laraba da daddare
  • Sai dai har yanzun babu wani bayani dangane da an biya kuɗin fansan da ɓarayin suka nema ko ba'a biya ba

Shugaban kwalejin koyar da aikin noma da kiyon dabbobi dake Bakura, Habibu Mainasara, ya samu kuɓuta daga hannun yan bindiga.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Zai Ƙaddamar da Wani Muhimmin Aiki Na Biliyoyin Naira Bayan Shekara 40 da Fara Shi

Ɗan uwan shugaban kwalejin, Nasiru Mainasara, ya shaidawa channels tv cewa an sako ɗan uwan nasa ne ranar Laraba da daddare, kwanaki uku bayan an sace shi daga gidansa dake makarantar.

Babu wani cikakken bayani dangane da yanda ya samu kuɓuta, yayin da ɗan uwansa yaƙi bayyana an biya kuɗin fansa ko ba'a biya ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Yan bindiga sun sako shugaban kwalejin fasaha
Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Sako Shugaban Kwalejin Fasaha a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɓarayin sun nemi naira miliyan N5m

A ranar Litinin kwana ɗaya bayan an sace shi, yan bindigan suka nemi a basu naira miliyan N5m a matsayin kuɗin fansa daga iyalinsa, daga nan suka cigaba da tattaunawa.

Sai dai ɗan uwan nasa ya bayyana cewa wasu manyan masu faɗa a ji na yankin sun faɗa wa iyalan shugaban da su dakatar da tattaunawa da ɓarayin kuma suka tabbatar da za'a sako shi cikin ƙoshin lafiya.

Bayan sace shugaban Kwalejin, rundunar yan sanda ta tura jami'an bincike da kuɓutarwa yankin domin binciko maharan kuma su kuɓutar da shi.

KARANTA ANAN: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, yace:

"Bamu da labarin an fara tattaunawa tsakanin iyalan shugaban kwalejin da kuma masu garkuwa da mutanen da suka sace shi."

A wani labarin kuma Yan Ta'addan da Luguden Wutar Sojoji Ya Koro Suna Tattaruwa a Yankunan Jihata, Gwamna Ya Koka

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari Baki Ɗaya Saboda Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya koka cewa yan bindigan da sojoji suka koro na taruwa a wasu yankunan jiharsa.

Gwamnan ya yi kira ga rundunar sojin sama da ta kafa sansanin sojinta a Kogi, don samun damar gano shirin yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262