Yan Ta'addan da Luguden Wutar Sojoji Ya Koro Suna Tattaruwa a Yankunan Jihata, Gwamna Ya Koka
- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya koka cewa yan bindigan da sojoji suka koro na taruwa a wasu yankunan jiharsa
- Gwamnan ya yi kira ga rundunar sojin sama da ta kafa sansanin sojinta a Kogi, don samun damar gano shirin yan ta'addan
- Shugaban rundunar sojin sama ya yaba wa gwamnan bisa ƙoƙarin kare al'ummar jiharsa
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya bayyana cewa yan bindigan da sojoji suke koro wa daga yankin arewa maso gabas suna ƙara taruwa a jihar Kogi, kamar yadda this day ta ruwaito.
KARANTA ANAN: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
Saboda haka gwamna Bello ya yi kira ga jami'an sojin sama da su kafa sansanin su a jihar domin yaƙar yan ta'addan, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Gwamna Bello, yace: "Yan bindigan da suke gudowa daga luguden wutan sojoji a yankin arewa maso gabas da arewa maso yamma suna sake taruwa a yankin Lokoja da Kabba/Bunu."
Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa
"Yanayin rashin tabbas a wannan yankunan ya sanya mutanen wajen sun fara canza matsuguni zuwa wasu sassan jihar."
Sansanin sojojin sama NAF
Gwamnan ya ƙara da cewa idan aka samar da sansanin sojojin sama NAF a jihar, zai matuƙar taimakawa wajen gano shirin yan bindigan.
Mr. Bello yace gwamnatin jihar Kogi ta miƙa ƙoƙon bararta ga rundunar NAF a shekarar 2017 domin ta duba yuwuwar kafa rundunar ko ta kwana a Zargi, yankin Lokoja.
A jawabinsa, shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya yaba da ƙoƙarin gwamnan na gano shirin da yan ta'adda suke yi a jiharsa, da kuma ƙoƙarin kare jihar Kogi.
KARANTA ANAN: COVID19: Wata Jami'a Ta Umarci Dalibai Su Koma Gida Har Sai Baba Ta Gani
Amao ya tabbatar wa gwamnan da kudirin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na kawar da duk wasu yan ta'adda a Najeriya.
A wani labarin kuma Cikakken Bayani, Dan Majalisa na Shida Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa Jam'iyyar APC
Ɗan majalisar wakilan tarayya, Kabiru Amadu, daga jihar Zamfara ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC.
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya karanta wasiƙar Amadu a zaman majalisar na Laraba.
Asali: Legit.ng