Da Ɗuminsa: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Da Ɗuminsa: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

  • Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana kudirinsa na rushe wani yanki baki ɗaya
  • Wani bincike ya nuna cewa gaba ɗayan yankin ya zama matattarar yan ta'adda
  • Gwamnan ya kai ziyara domin ya gane wa idonsa yankin, wanda ake wa laƙabi da Remon Village

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya sanar da ƙudirinsa na rushe wani wuri da ake kira Remon Village, wanda yake ɓoye duk wasu kalan yan ta'adda a jihar Sokoto.

KARANTA ANAN: Bayan Komawarsa PDP, Gwamna Ya Sha Alwashin Ba Zai Taɓa Komawa Jam'iyyar APC Ba

Wannan ya biyo bayan wani bincike da jaridar dailytrust ta gudanar kuma ta buga shi ranar Lahadi.

Binciken ya tona asirin duk wasu ayyukan ta'addanci na karya dokar ƙasa da ake aiwatar wa a wannan yankin.

Kauyen Reymon
Da Ɗuminsa: Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna Tambuwal, wanda ya ziyarci yankin da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Talata, yace mafi yawancin mazauna yankin suna rayuwa ne a wurin ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal na shirin yin rusau a kauyen Remon da ke jihar Sokoto

Jami'an tsaro sun mamaye wurin inda suka kame aƙalla mutum 100 da ake zargi da aikata wasu laifuka.

Jami'an tsaron sun haɗa da sojojin ƙasa, Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, hukumar NSCDC, hukumar kare haɗurra ta ƙasa, duk bisa jagorancin rundunar yan sanda.

An kai waɗanda aka kama hedkwatar yan sanda

An kai mutanen da ake zargin zuwa Hedkwatar rundunar yan sandan jihar Sokoto, inda aka tsare su a sashin binciken laifuka.

Rahotanni sun bayyana cewa har da mata a cikin waɗanda aka kame ake zargi.

KARANTA ANAN: Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi

Da yake tabbatar da lamarin ga manema labarai, kakakin yan sandan jihar, ASP Sanusi Abubkar, yace an kama mutum 144, kuma an kwato ƙwayoyi da dama.

"Zamu bincike su baki ɗaya, kuma duk wanda aka kama da laifi, zai fuskanci hukunci," inji shi.

Kara karanta wannan

Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

A wani labarin kuma An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu

Yan bindiga sun kaiwa ɗaliban jami'ar jihar Delta hari yayin da suke kan hanyarsu ta komawa makaranta.

Maharan sun kashe ɗalibi ɗaya, Odje Stephen, sannan suka yi awon gaba da wasu guda biyu, Jennifer da Divine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel