Manyan yara sun yi ruwan kudi a wajen wani liyafar biki da aka yi a Benin

Manyan yara sun yi ruwan kudi a wajen wani liyafar biki da aka yi a Benin

  • Wasu manyan yara a jihar Edo sun nuna cewa akwai kudi a kasar duk da cewar mutane na korafin rashin kudi
  • An ga yaran suna watsa kudi a sama a wurin bikin aure sannan kuma suka yi wa mahalartan bikin kyautar kudi
  • 'Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun mayar da martani game da bidiyon, inda wasu ke tambayar ina samarin ke ganin kudi a lokacin da gari yayi zafi

Wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu manyan yara suna jefa kudi a sama a wajen wani bikin aure a Benin, babban birnin jihar Edo.

Yaran sun fito da damin kudi masu yawa inda suka dunga jefa su a iska sannan kuma an gano baƙi da suka hallara suna ta dibar rabonsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda 73, ta ceto mutum 55 a Borno

Manyan yara sun yi ruwan kudi a wajen wani liyafar biki da aka yi a Benin
An gano samarin suna ta watsa bandir-bandir na kudi a sama Hoto: @instablog9ja
Asali: Instagram

A bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram ta @instablog9ja, an ga yaran ma a filin suna ta yi wa wasu baƙi liki yayin da kudade suka cika filin.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayinsu a kan bidiyon

@gee_prince1 ya yi tsokaci:

"Babu abin da ya damu samarin benin game da abin da ke faruwa a Najeriya a yanzu, har yanzu suna samun kudinsu hankali kwance."

@didi_ratti yayi tsokaci:

"A ina kuke ganin wannan kudin", bani da ko sisi", "babu kudi a kasa". Dukkanin su suna nan."

@literxchange ya ce:

"Me ya sa suke kwashe kudi a bikin wani?"

@baudex yayi sharhi:

"Sun kwashe kudin mai biki fa.”

Diyar biloniya Aliko Dangote ta birge masoya da takun rawanta

A wani labarin, diyar mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, Halima ta shiga kanen labarai kuma ta birge masu amfani da shafukan intanet.

Matashiyar matar wacce kan birge masoya da rashin hayaniyarta ta ba mutane da dama mamaki bayan ta fito ta yi rawa a wani taro da ta halarta.

Sabanin yadda aka saba ganinta, matashiyar ta sha rawa a filin taro yayinda take rera wakar da ke tashi na shahararriyar mawakiya, Teni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel