An yi aure a Asabar, Ma’aurata sun yi hadari a Talata, za a birne Miji a ranar Laraba
- A karshen makon nan Jamilu Abdulhamid Girei ya auri Saratu Salisu Abdul
- Yanzu maganar da ake yi, an sa lokacin jana’izar Jamilu Abdulhamid Girei
- Angon ya rasu a hadarin mota, ita amaryar ta sa na kwance a gadon asibiti
An daura aure ranar Asabar
A ranar Asabar da ta gabata, 11 ga watan Yuli, 2021, wani Bawan Allah mai suna Jamilu Abdulhamid Girei ya auri sahibarsa, Saratu Salisu Abdul.
Kamar yadda muka samu labari, an daura wannan aure a unguwar Goron Dotse da ke cikin birnin Kano.
Abin da babu wanda ya sani a Duniya shi ne saura kwana biyu wadannan sababbin ma’aurata su gamu da hadarin da zai dauki ran Jamilu Abdulhamid Girei.
KU KARANTA:'Yan Hisbah sun cafke 'Yan Luwadi a Kano
Hadarin mota ranar Talata
Malam Jamilu Abdulhamid Girei da amaryarsa sun yi hadarin mota ne a kan hanyar zuwa Abuja.
Wani wanda ya san ma’auratan, Kabiru Garba ya bayyana yadda abin ya auku, a shafinsa na Facebook, ya ce yanzu haka amaryar ta na jinya a gadon asibiti.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Mun rasa Jamilu a mummunan hadarin mota, a hanyarsu ta zuwa Abuja.
Ma’auratan sun yi aure ne ranar Asabar da ta gabata, su ka bar Kano zuwa Abuja inda za su zauna a gidansu a Jamhuriyyar Benin.
KU KARANTA: An kama dillalin IPOB da kwayoyin N150m
Na yi magana da Saratu karshe a jiya (ranar Lahadi), inda ya sake taya ta murnar auren da ta yi. A halin yanzu Saratu ta na asibiti, likitoci suna duba ta.
Allah ya jikanshi da rahma, ita kuma Allah ya ba ta lafiya."
Asalin wannan amarya mutumiyar Kaduna ce, amma ta na zama a garin Kano har zuwa jiya. Za a birne marigayin a unguwar shagari quarters, Kano an jima.
Ibrahim El-Caleel ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa lallai Duniya ba mattaba ba ce, ya yi wa wanda ya rasu addu’a, tare da rokon Allah ya ba matar lafiya.
Asali: Legit.ng