Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin korona kashi na biyu

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin korona kashi na biyu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi allurar rigafin korona ta AstraZeneca kashi na biyu

- Buhari kasar ya karbi allurar ne a fadar Shugaban kasa, Abuja, a yau Asabar, 29 ga watan Mayu

- Fadar shugaban kasar ce ta tabbatar da hakan a wani wallafa da tayi a shafinta na soshiyal midiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amshi allurarsa ta rigafin korona wato AstraZeneca COVID-19 kashi na biyu.

Shugaban kasar ya karbi allurar ne a gidansa da ke fadar Shugaban kasa, Abuja, a yau Asabar, 29 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Hatsarin jirgin soji: NAF ta bayyana dalilin da yasa aka kyale kananan matuka suna jigila da COAS da sauransu

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin korona kashi na biyu
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya karbi allurar rigakafin korona kashi na biyu Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Fadar Shugaban kasar c eta tabbatar da hakan a wani wallafa da tayi a shafinta na Twitter.

Anyi kashi na biyun ne makonni 12 cif bayan ɗaukar farko a ranar 6 ga Maris.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Babban likitan Shugaban kasar, Dakta Suhayb Rafindadi Sanusi ne ya yi wa shugaban sabon alluran inda bayan an gama sai shugaban darakta na Hukumar Kula da Kiwon Lafiya ta Kasa, Dakta Faisal Shuaib ya ba shi katin rigakafin.

Legit.ng ta zakulo wasu daga cikin martanin yan Najeriya kan haka:

@omasonamicable ya ce:

Shin matsalar Najeriya yanzu ta raba alluran rigakafin korona ce, wannan gwamnatin koyaushe tana mayar da hankali ga abubuwa marasa amfani saboda suna so su kwashi ganima daga can, duk wannan 'yan Najeriyar da ba su ji ba basu gani ba suna mutuwa a kulla yaumin shin korona ce ke kashe su, wannan gwamnatin tana son kuɗi fiye da rayuwa.

@ PetersonGlobal3 ya ce:

Ya kamata ku daina yaudarar yan Najeriya, Shugaban kasar da ya tashi zuwa #London don jinya yana kokarin yaudarar mu da karbar rigakafin COVID-19 a Najeriya? Mr. @Mbuhari, mun gode da bude mana idanunmu da kunnuwanmu.

@ AbdullahiLabou5 ya ce:

Hmmmm wannan na rigakafin zazzabin cizon sauro ne ba rigakafin korona bane.

A gefe guda, an bayyan shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe lambar yabon "Gwarzon mai gina hanyoyi 2021' wacce akewa laƙabi da Trophée Babacar Ndiaye, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Najeriya ya ƙwace kyautar ne daga hannun shugaban ƙasar Egypt, Abdul Fatta Al-sisi wanda ya lashe kyautar a shekarar 2020.

A jawabin da bankin Africa AfDB ya fitar jiya, yace an bayyana sunan Buhari a matsayin wanda ya lashe kyautar a wajen buɗe taron masu gina hanyoyi ranar 31 ga watan Maris a Cairo, Egypt.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng