Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

  • Wani soja da ya fusata ya sheke masoyiyarsa saboda zargin ta yaudareshi da kuma takaici
  • Ya ce ya bayyana wa mahaifiyar budurwar cewa, kawaye na daurata a kan mummunar hanya
  • Rundunar 'yan sanda ta ce tana bincike cikin tsanaki don tabbatar da adalci a cikin lamarin

Daga jihar Bayelsa - Wani soja mai tsananin kishi James Matol ya harbe wata mace mai suna Miss Jennifer Agadu har lahira, wata dalibar aji biyu a jami'ar Neja Delta, Amassoma dake jihar Bayelsa.

Jami’an tsaro dake aiki a jami'ar sun ce an gano gawar dalibar mai shekaru 21 a jiya da raunin harsashi da kuma yatsan hannu a yanke. Babban dan yatsa ma ya kusan yankewa, lamarin da ya nuna cewa sunyi gwagwarmaya.

An ba da rahoton cewa an ga dakinta a warwatse kana yana cike da jini, The Nation ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Gwamnan Gombe ya bayyana matakan da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Kara karanta wannan

Kananan hukumomi biyu ne kawai ke cikin aminci a Kaduna - Sanata Sani

Kishi ba sai mata ba: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi
Soja da Masoiyarsa da ya kashe | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Matol, wanda aka bayyana a matsayin masoyinta, an zarge shi da kashe ta bayan da ya yi zargin ta daura wasu kalamai a shafinta na WhatsApp wadanda basu mishi dadi ba, yana mai cewa ya kashe ta ne saboda yaudararsa da kuma takaicin da ya ji.

Wata kawarta ta bi cikin wayarta inda ta yi tuntube da sakonnin Whatsapp daga Matol inda ya zarge ta da yaudararsa kuma ya yi barazanar kashe ta kafin ya kashe kansa, in ji jaridar Sun.

Sojan ya kuma yi ikirarin cewa ya sanar da mahaifiyar Jennifer wacce ta kasance kanwar mahaifinsa kan abinda ya aikata da kuma cewa kawayenta biyu Vera da Eniye ba su daurata kan kyakkyawar shawara.

Kwamishanan 'yan sanda Mike Okoli ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin tsanaki game da lamarin.

Kasar Larabawa ta kirkiri manhajar soyayya don hada aure daidai da tsarin Muslunci

A kasashen ketare kuwa, mahukunta a kasar Iran sun kaddamar da wata manhaja ta soyayya wadda suka ce nufinta shi ne ta saukake neman aure bisa tsarin addinin Musulunci, BBC Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

Hukumar yada manufofin addinin Musulunci ta kasar ce ta kirkiro manhajar mai suna Hamdam wadda ke nufin aboki ko abokiyar zama, AlJazeera ta ruwaito makamancin haka.

Manhajar tana amfani da basirar komfuta wajen hada wadanda suke son su yi aure, kodayake mata daya kacal aka amince wa namiji ya aura.

KARANTA WANNAN: Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata luwadi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso.

Shugaban hukumar Harun ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, BBC ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta tattaro, a cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

Kara karanta wannan

COVID-19: Yadda Najeriya ta kunyata masana - Aregbesola

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.