Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Nigeria kasa ce mai sa'a shi yasa duk da kallubalen da ta fuskanta bata rabe be
  • Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya kai masa rahoton tsaro
  • Buhari ya kuma shawarci shugabanni su rika mutunta al'umma ta hanyar barinsu su zabi wadanda suke son su jagorance su

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya ce Nigeria ta yi matukar sa'a duba da cewa kallubale masu wahala da ta ci karo da su basu raba kasar ba, Daily Trust ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati a Abuja, yayin da ya ke karbar rahoton taron tsaro na kasa da Majalisar Wakilai na tarayya ta yi a ranar 26 ga watan Mayun 2021.

Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta
Buhari: Mun Yi Sa'a Nigeria Bata Rabu Ba Duk Da Ƙallubalen Da Muke Fuskanta. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi

Tawagar mambobin yan majalisar wakilai na tarayya karkashin jagorancin kakakin majalisa Femi Gbajabiamila ne ta kai wa Buhari rahoton.

Shugaba Buhari ya ce:

"Nigeria kasa ce mai sa'a kuma ya kamata mu taya kanmu murna, duk da kallubalen da muka fuskanta ba mu rabu ba."

Buhari ya shawarci shugabanni su rika mutunta jama'a

Shugaban kasar cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar ya bukaci shugabanni su rika mutunta ra'ayin mutane, daga kasa har sama, 'hakan zai sa mutanen su rika mutunta shugabannin suma.

Mutunta mutane, a cewar shugaban shine 'kyallesu su zabi wadanda suke so a matsayin shugabannin su, ba tare da la'akari da jam'iyya ko addini ba.'

Shugaba Buhari wanda ya bayyana taron a matsayi 'lamari mai muhimmanci' ya jadada niyyarsa na yi wa kasar hidima iya bakin kokarinsa.

Zamfara: Ba za mu bari abin da ya faru da APC a 2019 ya sake faruwa ba, Yeriman Bakura

Kara karanta wannan

Tun kafa Najeriya, ba a taba mulki mai kyau kamar na Buhari ba, gwamna Masari ya bayyana dalili

A wani labarin daban, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma mai neman takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sani Yerima, ya ce masu ruwa da tsaki a siyasar jihar za su haɗa kai don ganin ba a maimaita abin da ya faru a 2019 ba, rahoton Daily Trust.

Kotun koli ta soke kuri'un APC a zaben 2019 a jihar Zamfara don jam'iyyar bata da ikon tsayar da ƴan takara don bata yi zaben fidda gwani ba yadda ya dace.

A hirar da ya yi da manema labarai a karshen mako a Abuja, Yerima ya ce babu rikici a jam'iyyar APC ta Zamfara kan shigowar Gwamna Bello Matawalle cikin jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel