Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna

Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna ta fitar da rahoton adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin yan bindiga cikin watanni uku
  • Ma'aikatar tsaro da al'amuran cikin gida ta bayyana cewa an kashe mutum 222 da yan bindiga 87
  • Rahoton ya nuna cewa jam'an tsaro sun samu nasarar kame yan bindiga 24 a tsawon wannan lokacin

Wani rahoto da ma'aikatar tsaro da al'umuran cikin gida ta fitar ya nuna cewa aƙalla mutum 222 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren yan bindiga da rikice-rikice a jihar Kaduna daga watan Afrilu zuwa Yuni na 2021.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Dumi: An Kuma, Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗalibin wata Jami'a, Sun Yi Awon Gaba da Wasu

Hakanan kuma rahoton ya gano cewa maharan sun yi garkuwa da mutum 774, daga cikinsu 239 mata ne da kuma ƙananan yara 32, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.

Hakazalika daga cikin waɗanda aka kashe akwai mata 9 da ƙananan yara 8, sannan an jikkata mutm 266 a cikin watanni uku, 18 mata da kuma ƙananan yara 5, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara

Rahoton harin yan bindiga cikin wata uku a Kaduna
Wani Rahoto Ya Bankaɗo Adadin Mutane da Yan Bindigan da Aka Kashe Cikin Watanni 3 a Jihar Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jami'an tsaro sun kashe yan bindiga da dama

A ɓangaren jami'an tsaro kuma, rahoton ya bayyana cewa an samu nasarar hallaka yan bindiga 87 waɗanda ake zargin yan fashi da makami ne.

Wani sashin rahoton, yace: "Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka yan bindiga 87, yayin da aka kame mutum 24 cikin watanni uku."

Rahoton ya kuma ƙara da cewa yan fashin sun yi awon gaba da shanun mutane kimanin 8,553 a wannan lokacin.

KARANTA ANAN: Bayan Ɗalibai Sun Faɗi Jarabawar UTME 2021, Sanatoci Zasu Yi Garambawul a Wasu Dokokin JAMB

Jimulla dai, rahoton da gwamnatin Kaduna ta fitar ta hanyar ma'aikatar tsaro da al'amuran cikin gida ya bayyana cewa daga 1 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Yuni an kashe mutum 222 da yan bindiga 87.

A wani labarin kuma Gwamna Ya Sha Alwashin Rushe Wani Gari dake Ɓoye Yan Ta'adda a Jiharsa

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya sanar da ƙudirinsa na rushe ƙauyen Reymon, wanda yake ɓoye duk wasu kalan yan ta'adda a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an tsaro sun ceto wasu da aka sace ciki har da dalibin makarantar Bethel

Gwamna Tambuwal, wanda ya ziyarci ƙauyen da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Talata, yace mafi yawancin yan ƙauyen suna rayuwa ne a wurin ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel