Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya

  • Gwamnati za ta fara duba abinda yan Najeriya ke tattauna a wayoyinsu
  • Hakazalika an ware da makudan kudade na musamman domin haka
  • Masu sharhi sun ce wannan kutse ne cikin yancin dan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ajiye kimanin bilyan 4.8 ga hukumar leken asirin Najeriya (NIA) domin bibiyan abubuwan da yan Najeriya ke tattaunawa a WhatsApp da kuma salular Thuraya.

WhatsApp wata manhaja ce da mutane ke tattaunawa da 'yan uwa da abokan arziki.

WhatsApp mallakin kamfanin Facebook ne dake jihar California a Amurka.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa wannan kudi na cikin sabon karin da akayi cikin kasafin kudin 2021.

KU DUBA: Magoya bayan Buhari ba za su taba barin Tinubu ya zama Shugaban Kasa ba – Lamido

Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya
Gwamnatin tarayya ta kebance kimanin bilyan 5 don bibiyan Whatsapp din yan Najeriya
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Mune kurar baya a kowane bangare, kuma ba mu da ilimi: A cewar wata ‘yar Arewa cikin bidiyo

A ranar Laraba, majalisar dokokin tarayya ta amince da karin N982 billion cikin kasafin kudin 2021.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Yarbawa sun gabatarwa Majalisa jerin sababbin bukatu 6 da suke da su a Najeriya

Daga ciki za'a yi amfani da N123Billion matsayin kudaden albashi da saye-saye, sannan N895bn wajen manyan ayyuka.

Hukumar yan sanda ya samu N33.6bn, ma'aikatar tsaro ta samu N1.6bn domin daukan sabbin soji 2,700.

Hukumar DSS ta samu N17.5bn don sayen motoci, makamai dss.

An ware N60.7bn don sayen rigakafin COVID-19, an ware 20bn don rabawa asibitoci.

'Yan bindiga sun bankado rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN

Wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Litinin sun bayyana yadda ‘yan bindiga ke dakile matakan tsaro na Gwamnatin Tarayya a bangaren sadarwa.

Mazauna jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna wadanda suka ba da labarin irin abubuwan da suka fuskanta a wuraren da masu satar mutane suke, sun shaida wa manema labarai cewa sun bai wa jami’an tsaro lambobin wayar ‘yan bindigar.

Sai dai sun koka cewa, duk da hakan babu wani abin da aka yi domin kama miyagun, hakan ya sa ake ganin umarnin Gwamnatin Tarayya kan rajistar masu amfani da wayar tarho da kuma lambar shaidar kasa a zaman shiririta ce kawai.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel