Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi

Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi

  • Dandazon mutane a Kajuru sun fito don nuna tsantsar farin cikinsu da dawowar sarkin su jim kaɗan bayan an sako shi
  • A ranar Litinin da yamma, yan bindiga suka sako sarkin awanni bayan sun sace shi tare da wasu mutum 13
  • Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, ya koma cikin masarautarsa, amma yadda aka tarbe shi sai da ya sa shi hawaye

Yammacin ranar Litinin yazo wa jama'ar Kajuru da daɗi yayin da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Damu, ya dawo cikin mutanensa bayan ɗaukar awanni sama da 24 a hannun masu garkuwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken ne da sanyin safiyar ranar Lahadi da ta gabata, kamar yadda punch ta ruwaito.

Da farko sun nemi a basu miliyan N200m kuɗin fansa kafin su sako shi, amma awanni kaɗan bayan haka sai ga basaraken ya dawo cikin masarautarsa a jihar Ƙaduna

Kara karanta wannan

Yariman Kajuru ya bayyana abinda 'yan bindiga suka sanar masa kafin sakin mahaifinsa

Amma abin takaicin shine, 'yayansa, jikokinsa, da wasu mutane dake da muƙamai a masarautar, waɗanda aka sace su tare, har yanzun suna hannun ɓarayin.

Mutane sun ɓarke da murna da farin ciki

Sai dai dandazom jama'an Kajuru sun nuna tsantsar farin ciki da murna yayin da suka ga sarkin su ɗan kimanin shekara 85 ya dawo garesu.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Nnamdi Kanu

Basaraken yayi ƙoƙarin jawabi a gaban jama'a amma saboda murnar yadda aka tarbe shi bai iya ƙarisa zancen da yayi niyya ba.

Dandazon mutanen Kajuru
Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutanen Kajuru sun ɓarke da murna
Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mutane na murna da farin ciki
Hotunan Yadda Dandazon Mutane Suka Sanya Sarkin Kajuru Hawaye Jim Kaɗan Bayan an Sako Shi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sarkin ya fara magana da "Mutanen Kajuru...." amma sai ya kasa ƙarisa wa, sai hawaye suka zubo masa.

A wani labarin kuma Cikakken Bayani: Dalilin da Yasa Shugaban Izala na Kano Ya Kai Ƙarar Sheikh Abduljabbar Kabara

Rundunar yan sanda a Kano ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Wannan na zuwa kwana biyu kacal da malamin yayi muƙabala da wasu malaman jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel