Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara
- Luguden da sojojin sama suka yi wa sansanin 'yan bindiga ya janyo mutuwar 120 daga ciki
- Sojin saman Najeriyan sun ragargaji 'yan bindigan a maboyarsu dake dajin Sububu, Zamfara
- Lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan bayanan sirrin da jami'an tsaro suka samu
A kalla miyagun 'yan bindiga 120 ne suka sheka barzahu sakamakon luguden ruwan wuta da sojojin sama suka yi wa 'yan ta'addan a dajin Sububu dake jihar Zamfara.
An kaddamar da luguden a ranar Litinin bayan wasu mazauna yankin sun sanar da jami'an tsaro sauka da kaiwa da kawowar 'yan bindiga masu tarin yawa a kusa da Sububu.
Wani jami'in sirri ya sanar da PRNigeria cewa an tura jirgin yaki domin dubawa tare da tattaro hotuna da kuma duba yadda 'yan bindigan ke al'amura kafin a kaddamar da harin.
KU KARANTA: Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno
KU KARANTA: Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama
"Bayan bayanan sirri na kaiwa da kawowar 'yan bindiga a dajin Sububu, Jajani da Dammaka, jirgin yawo ya leka inda ya duba yanayin yankin kafin a kaddamar da luguden wutan.
"Kamar yadda ya dace, jiragen yaki sun mamaye wurin inda suka dinga luguden wuta a yankin kudu maso yamma na Sububu.
“Yan bindigan da suka sha da kyar sun tsere daga yankin. An yi ittifakin a kalla 'yan bindiga 125 ne aka halaka a farmakin sakamakon bayanin da aka samu daga yankin," yace.
Mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da nasarar inda yace sun ragargaji maboyar 'yan bindigan tare da wasu baburansu.
Amma kuma bai bada karin bayani kan mutanen da suka rasa rayukansu ba, Leadrership ta ruwaito.
A wani labari na daban, wani dan gidan sarautar Kajuru da ya bukaci a boye sunansa ya bada labarin gamonsu da 'yan bindigan da suka sace mahaifinsu, Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru a ranar Lahadi.
Daily Trust ta ruwaito yadda miyagun 'yan bindiga suka yi awon gaba da sarkin tare da wasu 13 daga cikin iyalansa bayan sun kutsa gidansa a ranar Lahadi.
Amma kuma an sako shi a ranar Litinin yayin da 'yan bindigan suka bar sauran a hannunsu. Majiyar wacce take daga cikin tawagar da taje karbo sarkin, ta ce 'yan bindgan sun kira su ta wayar sarkin bayan sallar la'asar kuma sun ce su shirya karbarsa.
Asali: Legit.ng