Sunana Sarkin Hauka: 'Yan sanda sun kwamushe wani mai haukan gangan

Sunana Sarkin Hauka: 'Yan sanda sun kwamushe wani mai haukan gangan

  • Wani matashi ya shiga hannun 'yan sanda saboda yin shiga irin ta mahaukata a jihar Legas
  • Ya ce sun kama shi ne lokacin da yake cikin mota a hanyar ta zuwa wani wasan kwaikwayo
  • A cewarsa, shi ba mai aikata laifi bane, kuma ba matsafi ba, amma sun kama sun tsare shi

Wani matashi da ya bayyana kansa a matsayin Sarkin Hauka ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda na jihar Legas.

Da yake magana da jaridar Punch a yayin da aka cafke shi, matashin ya bayyana cewa sauka a ofishin ‘yan sanda wani abu ne da yake da matukar wahalar gaskatawa a gareshi.

Ya ce an kama shi ne bayan wasu ‘yan sanda sun tsayar da motar Uber da ya hau kan hanyarsa ta zuwa wani wasan kwaikwayo a Lekki da misalin karfe 10:45 na dare.

KARANTA WANNAN: Bayani: Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan ‘yar Najeriya da ta yi wuf da wani Bature, jama’a sun yi cece-kuce

Sunana Sarkin Hauka: 'Yan sanda sun kwamushe wani mai haukan gangan
Sunana Sarkin Hauka a hannun 'yan sanda | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa aka kawo shi ga ofishin, Sarkin Hauka ya ce:

“Har yanzu ban sani ba.
“Sun fada min cewa za su kai ni in hadu da wani DPO. Na ga kaina a nan da safiyar yau. Har yanzu ban fahimci abin da ke faruwa ba."

Ya bayyana cewa ba a samu wani abu na laifi a kansa ba, ya kara da cewa 'yan sandan sun ba shi izinin daukar bidiyo yayin da suka kame shi.

Sarkin Hauka yayin da yake cire rigarsa don bayyana jikinsa da ke cike zane-zane, ya ce:

"Shiga ta ta yi kama da na mai laifi, amma ni mai mawaki ne, ba mai matsafi ba."

Ya ci gaba da cewa:

“Babata ta kasance tana fada min cewa akwai wani lokaci da littafi zai zama kamar kazanta sosai da ba za ka iya taba shi ba balle ku gano abinda ya kunsa.

Kara karanta wannan

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

"Suna hukunta ni da kamanni na."

Ya kara da cewa an kama shi shi kadai yayin da aka bar direban Uber din ya tafi.

Kishi: Wani soja ya fusata ya bindige masoyiyarsa saboda zafin kishi

Daga jihar Bayelsa - Wani soja mai tsananin kishi James Matol ya harbe wata mace mai suna Miss Jennifer Agadu har lahira, wata dalibar aji biyu a jami'ar Neja Delta, Amassoma dake jihar Bayelsa.

Jami’an tsaro dake aiki a jami'ar sun ce an gano gawar dalibar mai shekaru 21 a jiya da raunin harsashi da kuma yatsan hannu a yanke.

Babban dan yatsa ma ya kusan yankewa, lamarin da ya nuna cewa sunyi gwagwarmaya. An ba da rahoton cewa an ga dakinta a warwatse kana yana cike da jini, The Nation ta ruwaito.

KARANTA WANNAN: Hotuna: Buhari ya sake karya dokar Korona a bainar jama'a duk bullowar sabon nau'i

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

A wani labarin, Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata luwadi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso.

Shugaban hukumar Harun ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, BBC ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta tattaro, a cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.