Hotuna: Buhari ya sake karya dokar Korona a bainar jama'a duk bullowar sabon nau'i

Hotuna: Buhari ya sake karya dokar Korona a bainar jama'a duk bullowar sabon nau'i

  • Jiya ne shugaba Buhari ya gabatar da wata liyafar cin abinci da mambobin majalisar dokokin Najeriya
  • Hotuna daga wurin liyafar sun nuna shugaba Buhari ba tare da takunkumin fuska ba, lamarin da ya jawo cece-kuce
  • Shugaban a watan Janairu ya halarci wani taro, inda aka gansa ba tare da takunkumin fuska ba

Kwanaki kadan bayan da cibiyar kula da cututtuka ta kasa ta sanar da bullar sabon nau'in cutar Korona a Najeriya, an ga shugaba Buhari a wurin taro ba tare da takunkumin fuska ba, Punch ta ruwaito.

A yammacin ranar Talata ne shugaban kasar ya halarci liyafar cin abinci tare da mambobin majalisar dokokin kasa, wanda aka yi a dakin taro na Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Hotunan taron wanda mai taimakawa Shugaban Kasa na musamman kan Watsa Labarai, Buhari Sallau ya wallafa, ya nuna cewa Shugaban ya isa wurin ne da takunkumin fuskarsa amma daga baya ya cire shi a cikin dakin taron.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Bayan dogon cece-kuce, majalisa ta karbi rohoton gyara dokar zabe

KARANTA WANNAN: Dalla-dalla: Dalilai da suka sanya majalisar dattawa ta ki amincewa da nada Onochie a INEC

Hotuna: Buhari ya sake cire takunkumin fuska a cikin taro duk da gargadi kan Korona
Shugaba Buhari ba tare da takunkumin fuska ba a wurin liyafa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hotunan taron sun nuna Shugaban (ba tare da rufe fuska ba) yana ta harkarsa da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, wadanda dukkansu suka sanya nasu a fuskokinsu da kyau.

Ba wannan ne karon farko da Buhari ya taba cire takunkumin fuska ba

Yammacin Talata ba shi ne karo na farko da Shugaban kasa ya cire abin takunkumin fuskarsa a bainar jama'a ba; ya taba cirewa a watan Janairun 2021 a wani taro a garinsu na Daura, Jihar Katsina, duk da dama fadar shugaban kasa ta fadi dalilin da yasa ya cire, SaharaReporters ta ce.

Jam’iyyar PDP da ‘yan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta sun soki shugaban kasar saboda sabawa ka’idojin da suka wajabta amfani da takunkumin fuska a bainar jama’a don rage yaduwar Korona.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Kalli hotunan:

Hotuna: Buhari ya sake cire takunkumin fuska a cikin taro duk da gargadi kan Korona
Shugaba Buhari ba tare da takunkumin fuska ba a wurin liyafa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hotuna: Buhari ya sake cire takunkumin fuska a cikin taro duk da gargadi kan Korona
Shugaba Buhari ba tare da takunkumin fuska ba a wurin liyafa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KARANTA WANNAN: Majalisa ta yi waje da kudurin gwamnatin Buhari na samarwa jami'an kashe gobara bindigogi

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa 'yan majalisa yayin ganawarsu a wajen liyafa

A wani labarin, A yammacin jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da mambobin majalisar dokoki ta kasa, domin gudanar da wata liyafa.

Shugaban kasar ya tattauna da 'yan majalisu da sanatocin, yayin da ya bayyana wasu maganganu ciki har da yabo da ba da tabbaci da goyon baya a gwamnatinsa.

Hakazalika, jaridar Punch ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana matsalolin da kasar ke fuskanta, inda ya nemi goyon baya wajen magance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.