Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi ba - Bala Mohammed

  • Gwamna Bala Mohammed ya ce sam gwamnatinsa ba za ta sake bari miyagun mutane su yi tunga a Jihar Bauchi ba ta yadda za su hana jama’a zuwa gonakinsu
  • Ya ce gwamnatinsa ta kafa wata rundunar tsaro ta mafarauta da masu banga domin kare al’ummar jihar daga ’yan bindiga bisa izinin Sufeta Janar na ’Yan Sanda
  • Sannan ya yi gargadi kan masu sayar da burtalolin kiwon shanu da su guji hakan

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta bari miyagun masu aikata laifuka su mamaye jihar tare da hana mutanen jihar damar zuwa gonakinsu ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake yaba wa kungiyoyin ’yan banga a cikin jihar kan himmarsu da kuma hadin gwiwar da suke yi da jami'an tsaro domin dakile aikata miyagun laifuka a jihar. Ya ce ba don su ba, da 'yan bindiga sun mamaye jihar, rahoton DN.

Ya fadi hakan ne a lokacin da yake kaddamar da noman rani na bana da kuma sayar da takin zamani a wani bikin da aka gudanar a garin Soro da ke yankin Karamar Hukumar Ganjuwa a jihar.

DUBA NAN: Gwamnatin Tarayya za ta kara ciyar da Dalibai firamare miliyan 5 - Minista Sadiya

Gwamnan ya ce:

“Muna kira ga ’yan banga, musamman da yake nan ne helkwatar kungiyar ’yan bangar da suke kiran kansu ‘Babeli’. Yanzu haka na tattauna da shugabansu, wanda yake mai sunana ne, muna yaba wa sosai da abin da suke yi.
“Suna aiki tare da ’yan sanda da sojoji kuma muna son wannan hadin kan ya ci gaba da wanzuwa.
"Muna tabbatar wa mutanen Bauchi cewa ba za mu yi bacci ba sannan mu bar miyagu masu aikata laifuka su samu gindin zama har su kafa sansanoninsu a garuruwa ko yankunan karkararmu ba ta yadda ba za su bar jama’armu su je gonakinsu ba.
“Kalubalen namu ne. Ya kamata ku tabbatar da cewa babu wanda ya hana ku aiwatar da 'yancinku na walwala, musamman wajen neman abin da za ku ci da kanku ta hanyar zuwa gonakinku ba.”

Bala Mohammed
Ba zan bari ’yan bindiga su samu gindin zama a Bauchi - Bala Mohammed
Asali: Original

KU DUBA: Saboda kokarin da mukayi, mutane na ajiye ayyukansu na Ofis suna komawa gona: Buhari

An kafa Rundunar Mafarautar

Gwamnan ya kara da cewa sakamakon hakan ne ya sa gwamnati ta yanke shawarar kafa wani ayari na musamman da ya kunshi mafarauta da kungiyoyin banga tare da amincewar Sufeto-Janar na ’yan sanda.

Ya kuma ce gwamnati na samun hadin kan hukumomin tsaro. Ya shawarci kungiyoyin 'yan banga da su "nisanci yin gaba da juna da nuna son kai da yin abubuwan da suka shallake dokar aiki."

Ya kuma gargadi Jami’an gandun dajin a jihar da su daina sayar da burtalolin shanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng