Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata

Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya wa sanatocin kasar liyafar cin abincin dare
  • Za a yi taron ne a daren yau Talata, 13 ga watan Yuli, a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Za kuma su tattauna kalubalen da tsaron kasar ke fuskanta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci mambobin majalisar dattijai zuwa liyafar cin abincin dare a Fadar Shugaban Kasa a yau Talata, 13 ga watan Yuli da karfe 8 na dare.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaban kasar a zauren majalisar yayin fara zama, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro a Najeriya: Wasu 'yan bindiga sun kashe malamin addini a jihar Taraba

Yanzu Yanzu: Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatoci 109 a yau Talata
Shugaba Buhari ya shirya liyafar cin abincin dare tare da sanatocin kasar Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Lawan ya bukaci takwarorinsa da su zo bangaren majalisar dattijai ta kasa don tashi zuwa fadar Villa da karfe 7 na yamma.

Jaridar This Day ta kuma ruwaito cewa Shugaban kasar ya nemi ganawa da dukkanin sanatocin kasar guda 109 domin tattauna matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Wasikar ta zo kamar haka:

“Na rubuta don in sanar da Mai Girma Shugaban Majalisar Dattawa, cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai shirya liyafar cin abincin dare ga Sanatocin Tarayyar Najeriya a ranar Talata, 13 ga watan Yulin, 2021, da karfe 8:00 na dare.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa a 2023: Kungiyar Arewa ta yiwa Ohanaeze wankin babban bargo kan furucinta game da Yahaya Bello

"Wurin taron shine dakin taro na Banquet Hall, Fadar Shugaban Kasa, Abuja."

Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, Daily Trust ta ruwaito.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan tsohuwar hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta daga jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Majalisa tayi watsi da sunan Onochie a matsayin kwamishinan INEC

An yi watsi da sunan Onochie ne bayan duba rahoton kwamitin hukumar zabe mai zaman kanta na majalisar dattawa wanda yake samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel