Da Ɗuminsa: Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Nnamdi Kanu

Da Ɗuminsa: Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Nnamdi Kanu

  • Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta gana da Akanta janar na ƙasa kuma ministan shari'a, Abubakar Malami
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa Nnamdi Kanu ɗan Najeriya ne kuma bai fi ƙarfin doka ba, amma ya kamata a masa adalci
  • Malami yace gwamnatin yanzu tana bin doka sau da ƙafa, kuma ba zata yarda wani ya karya doka ba

Tawagar shari'a na ƙungiyar Ndigbo sun gana da ministan shari'a kuma akanta Janar na ƙasa, Abubakar Malami, domin jin halin da ake ciki dangane da shari'ar shugaban ƙungiyar taware IPOB, Nnamdi Kanu, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin ofishin Akanta janar na ƙasa, Jibril Gwandu, ya fitar.

Jawabin ya bayyana cewa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana matsayarta game da Nnamdi Kanu, da cewa shi ɗan Najeriya ne kuma bai fi ƙarfin doka ta yi aiki a kansa ba.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Nnamdi Kanu da Malami
Da Ɗuminsa: Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Nnamdi Kanu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani sashin jawabin yace: "Ƙungiyar ta nuna ƙarara cewa ba ta da tunani irin na yan ƙungiyar IPOB yayin da ta bayyana cewa ba ta goyon bayan duk wani kalan tashin hankali."

"Ta kuma roƙi matasa da su zama masu bin doka sau da ƙafa, kuma su ta shi su mallaki katin zaɓe domin samun damar bada gudummuwa wajen cigaban ƙasa."

"Matsayar da ƙungiyar Ohanaezee ta ɗauka bai ci karo da doka ba kuma wannan abun a yaba musu ne."

Gwamnati na bin doka sau da kafa

Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa gwamnatin dake ci a yanzun tana matuƙar bin doka sau da kafa kuma ba ta sassauta wa wanda ya karya doka.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP

Ya ƙara da cewa ko akwai masu duba yanayin shari'ar ko babu, za'a yi adalci game da Nnamdi Kanu dai-dai da abinda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP

Ministan ya kuma nuna sha'awara cewa ƙungiyar ta cigaba da ƙoƙarin bin doka yayin da zasu isad da hukuncin kotu ga mutanen dake yankin su.

A wani labarin kuma Wani Babban Mai Faɗa a Ji a Jam'iyyar APC Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Wani babban jigon APC a jihar Gombe ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar zuwa PDP.

Muhammad Barde, wanda tsohon ɗan takarar gwamna ne a Gombe, yace APC ba ta iya shugabanci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel