Tsohon gwamnan Zamfara ya yi watsi da shawarar gwamnonin kudu, ya ce zai yi takara a 2023
- Tattaunawar 2023 ta dauki wani salo daban a baya-bayan nan biyo bayan kudurin Kungiyar Gwamnonin Kudancin kasar
- Kungiyar ta dage kan cewa lallai sai kudancin Najeriyar ta samar da magajin Shugaba Muhammadu Buhari
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima, ya ce zai tsaya takarar kujerar duk da matsayin kungiyar
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Ahmed Sani Yerima, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 duk da matsayar da kungiyar gwamnonin kudu suka dauka a baya-bayan nan.
Kungiyar a ranar Litinin, 5 ga watan Yuli, ta nace cewa ya kamata a mika shugabancin kasar ga yankin Kudancin Najeriya a 2023.
KU KARANTA KUMA: Kotun Abuja ta aika tsohon shugaban JAMB kurkuku, ta kuma bayyana dalilin yanke hukuncin
Yerima ya ce kudirinsa na da goyon bayan kundin tsarin mulki
Yayin da yake magana a Abuja tare da wasu ‘yan jarida, Sanata Sani ya ce ba zai yi watsi da kudirinsa ba tunda babu wani tanadi na mulkin karba-karba a kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma kudin tsarin mulkin jam’iyyar APC.
Jaridar Nigerian Tribune ta nakalto yana cewa:
"Duk wani dan Najeriya, a tsarin mulkin Najeriya, sai dai idan an yi masa kwaskwarima, yana da 'yancin ya nemi kowane irin mukami na siyasa da zarar ya cancanta. Ba za ku iya cewa wannan zagayena ne ba saboda batun zabe ne.
“Har yanzu muna da bambance-bambancen kabila da addini wanda ba shi da kyau. Kuma har sai zuwa lokacin da za mu yi imanin cewa mu ’yan Najeriya ne, to batun Hausa, Fulani, Ibo, Ijaws, mutane za su ci gaba.”
KU KARANTA KUMA: Hotuna sun bayyana yayin da gwamnonin arewa maso gabas suka isa Taraba don ganawa mai muhimmanci
A wani labari makamancin haka, kungiyar koli ta kabilar Ibo wato Ohanaeze Ndigbo ta aika sako ga gwamnonin kudu.
Sakon mai sauki ne - ya kamata shugaban kasa mai zuwa ya fito daga kudu maso gabas, jaridar Punch ta ruwaito.
Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta fadawa gwamnonin kudu cewa yankin kudu maso gabas ce ya kamata ta samar da shugaban kasa na gaba.
Yankin mu ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba, Gwamnonin Kudu
A wani labarin, Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 sun amince kan cewa shugaban kasar Nigeria na gaba a shekarar 2023 ya kamata ya fito daga yankinsu ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na dauke ne cikin sakon bayan taro da kungiyar gwamnonin kudun ta fitar bayan taron ta da aka yi a gidan gwamnatin Legas da ke Alausa, ranar Litinin.
Daily Trust ta ruwaito cewa sun kuma cimma matsayar cewa ya kamata a rika kama-kama ne tsakanin kudu da arewa wurin zaben shugaban kasar.
Asali: Legit.ng